Hatiya ( Bengali ) ita ce upazila, ko yanki, na Gundumar Noakhali a cikin Rukunin Chittagong, kasar Bangladesh. Tsibiri mai irin wannan suna yana cikin wannan upazila, kamar yadda Nijhum Dwip, wani ƙaramin tsibiri ne.

Hatiya Upazila

Wuri
Map
 22°22′N 91°08′E / 22.37°N 91.13°E / 22.37; 91.13
Ƴantacciyar ƙasaBangladash
Division of Bangladesh (en) FassaraChattogram Division (en) Fassara
District of Bangladesh (en) FassaraNoakhali District (en) Fassara
Yawan mutane
Faɗi 537,366 (2022)
• Yawan mutane 255.89 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 2,100 km²
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo ৩৮৯০
Wasu abun

Yanar gizo hatia.noakhali.gov.bd

Labarin kasa

gyara sashe
 
Tsibirin Hatiya a cikin 1778 a cikin taswira ta James Rennell

Hatiya Upazila tanada fadin wuri 22°22′00″N 91°07′30″E / 22.3667°N 91.1250°E / 22.3667; 91.1250 . sannan Tana da rukunin gidaje 47,970 da kuma jimlalar yanki na 2,100 murabba'in kilomita

Chars / Tsibiri

gyara sashe
  • Jahaijar Char

Yawan jama'a

gyara sashe

A ƙidayar Bangladesh a 2011, Hatiya tana da yawan jama'a kimanin mutane 442,463. Maza sun kai 51% mata kuma sun kasance 49%.Yawan mutanen da suka wuce shekaru 18 ya kasance 125,512. Hatiya tana da matsakaita na karance-karance na karatu na 69% (shekaru 7+), a kan matsakaita na ƙasa na 72.76%.

Tattalin arziki

gyara sashe

Upazila ya kunshi kasuwanni guda 52. Sun hada da Oskhali, Afazia, Tamruddi, Chowmuhani, Sagaria, Jahajmara, Sonadia chowrasta, Char Chenga, Maijdee Bazar da Nalchira Bazar. Yawancin mutane suna aiki noma da kamun kifi, kuma profan sana'oi na gwamnati ne ko na aikin gwamnati. Dukkanin bankuna suna karkashin gwamnati ne wadanda suka hada da Krishi Bank, da Sonali Bank Limited, da kuma Janata Bank Limited.

Babban kayan da ake fitarwa sun hada da: shinkafa, kwakwa, gyada, ayaba, ganyen bawon, chili, Hilsa, da sauran nau'ikan kifi.

Gudanarwa

gyara sashe

An raba Hatiya Upazila zuwa Karamar Hukumar guda da kuma mambobin kungiyar guda 11 Union.

Kamfanin Municipal:

An raba karamar hukumar Hatiya zuwa anguwanni guda 9 da mahallasi guda 23.

An raba majalisun kungiyar kwadagon zuwa mauza guda 44 da kauyuka guda 62.

  1. Burir Char
  2. Chandnandi
  3. Char Ishwar
  4. Char King
  5. Harni
  6. Jahajmara
  7. Nijhum Dwip
  8. Nolchira
  9. Sonadiya
  10. Sukhchar
  11. Tomoroddi

Kiwon lafiya

gyara sashe

Akwai Upazila Health Complex guda daya da kuma cibiyoyin tsara iyali guda 10. Sanannun kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a wannan yankin sune: bankin Grameeen, Dwip Unnoyan Songstha, Brac, Proshika, Heed Bangladesh, CARE, da Caritas.

Cibiyoyin ilimi mafi girma sun hada da: Kwalejin Gwamnati ta Hatiya Dwip da kwaleji uku masu zaman kansu.

Duba kuma

gyara sashe
  • Upazilas na Bangladesh
  • Gundumomin Bangladesh
  • Rabarorin Bangladesh
  • Jerin tsibiran Bangladesh

Manazarta

gyara sashe