Hassana Muhammad (An haife ta ranar 28 ga watan mayu, shekara ta alif 1997).Yar jahar Kaduna ce. Ta kasance shahararriyar yar wasan kwaikwayo ce a cikin masana`antar kannywood.[1] Ta shahara ne a fim din Hauwa kullu.

Farkon rayuwa da karatu gyara sashe

Hassana ta girma a garin Kaduna. Mahaifinta shine Alhaji Muhammad, sanannen dan kasuwa ne. Ta kammala karatun firamare da sakandare duk a garin Kaduna. daga bisani samu digiri a jami`ar jihar Kaduna[2]

Shahara gyara sashe

Hassana ta samu yin fice ne bayan muhimmiyar rawar da ta taka a cikin fim din Hauwa Kulu wannan fim yasa ta lashe kyautar City People Entertaiment award.

Aikin fim gyara sashe

Ta fara fitowa a fim dintana farko mai suna Mujadala, wand aciki akwai jarumi Umar M. Shareef. Sannan tayi fina-finai da dama ga wasu daga ciki;

  • Mujadala
  • Hauwa Kulu
  • Hafiz
  • Halimatu saadiya
  • Agola. da sauransu..

Iyali gyara sashe

Ta auri ɗan kasuwa kuma mai shirya fina-finai a masana`antar Kannywoood, wato Abubakar Bashir Maishadda

Manazarta gyara sashe

  1. https://ngsup.com/hassana-muhammad-biography-age-career-and-photos/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-04-21. Retrieved 2022-08-02.