Hassana Abdullahi Jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kannywood ta Dan jima a masana'antar tayi fina finai da dama a masana'antar tare da yar uwarta Hussaina.[1]

Tarihin gyara sashe

Cikakken sunan ta shine Hassana Musa Abdullahi , jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kannywood. An haifeta tare da yar uwarta hussaina a ranar 20 ga watan fabrairu shekarar 1995 a unguwa uku Karamar hukumar Tarauni a cikin jihar [2]kano. Sun girma ita da yar uwarta a cikin garin Kano,haka zalika su yaren Hausa ne da kuma Fulani .

Karatu gyara sashe

Jarumar tayi karatun firamare tare da yar uwarta hussaina a makarantar dake unguwa uku special primary school, sunyi karatun sakandiri a government girls secondary school Johanna a garin kano. Bayan ta gama hassana ta shiga kwalejin Aminu Kano inda tayi difloma ta Karanci Islamic and legal studies, inda ta gama a shekarar 2014.[3]

Masana'antar Fim gyara sashe

Hassana ta Sami shiga masana'antar ita da yar uwarta Hussaina ta hanyar abokin Hussaina na makaranta Wanda darakta ne a masana'antar. Farko Yana Kiran su suga yanda ake yin fim din daga Nan suke Sha,awan fim din. Sun shiga masana'antar fim a shekarar 2013.[4]

  • Fina Finan Ta
  • Juyin Mulki
  • fitsarin fako
  • Mairon kauye
  • Ibro Dan karota
  • duka biyu
  • Sabon Dan tijara

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.blueprint.ng/i-wont-wait-for-my-twins-if-i-get-suitor-hassana-musa-abdullahi/
  2. https://www.pressreader.com/nigeria/daily-trust-saturday/20160123/281702613727649
  3. https://hausa.legit.ng/1145901-kannywood-yadda-wasu-tagwaye-ke-sharar-fage-a-shirin-fim.html
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.