Harry Rabinowitz
Harry Rabinowitz MBE (26 Maris 1916 - 22 Yuni 2016) ɗan Afirka ta Kudu ne ɗan Burtaniya, mai shirya fim da kiɗan talabijin.[1] An haife shi a birnin Johannesburg, Afirka ta Kudu, ɗan asalin Isra'ila ne haka-zalika ɗan Eva Rabinowitz ne. Ya yi karatu a Jami'ar Witwatersrand da kuma Makarantar Kiɗa da Wasan kwaikwayo ta Guildhall ta London.[1]
Harry Rabinowitz | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Johannesburg, 26 ga Maris, 1916 | ||
ƙasa | Ingila | ||
Mutuwa | Lacoste, 22 ga Yuni, 2016 | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Witwatersrand Guildhall School of Music and Drama (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | mai rubuta kiɗa da conductor (en) | ||
Kyaututtuka | |||
IMDb | nm0704948 |
Sana'a
gyara sasheYa fara aikin waka a matsayin mai kiɗa a wani kantin sayar da kayayyaki na Johannesburg. Aikinsa na farko da ya jagoranci ƙungiyar makaɗa shine don wasan kwaikwayo mai suna Strike a New Note a 1945. Rabinowitz ya bar birnin Johannesburg zuwa Ingila a shekarar 1946 domin karantar nazarin gudanarwa.
Ya kasance shugaba na Orchestra na Revue na BBC (daga 1953 zuwa 1960), darektan kiɗa na BBC Television Light Entertainment (daga 1960 – 1968), kuma shugaban kiɗa na Gidan Talabijin na London Weekend Television (1968 – 77). [1] Haka-zalika a Hollywood Bowl (1983 – 84) da kuma Boston Pops Orchestra (1985 – 92) kuma tare da Orchestra na Symphony na London da Royal Philharmonic Orchestra. [1] Shi ne jagoran ƙungiyar Orchestra na St. Luke's Ismail Merchant da James Ivory bikin cika shekaru 35 a zauren Carnegie a ranar 17 ga watan Satumba 1996.[ana buƙatar hujja]
Rabinowitz ya shirya kidan bayan fage na finafinai da suka haɗa da;, Hanover Street (1979), Chariots of Fire (1981), Heat and Dust (1983), The Bostonians (1984), Return to Oz (1985), Lady Jane (1986), Maurice (1987), The Remains of the Day (1993), The English Patient (1996), The Talented Mr. Ripley (1999), da Cold Mountain (2003).[1] har wayau ya shirya wasu kidan ga shirye-shiryen shirin Talabijin, da suka haɗa da ;, The Frost Report (1966), I, Claudius (1976) da The Agatha Christie Hour (1982).Samfuri:Fact
Ya fito a shirin talabijin na Top C's and Tiaras.[ana buƙatar hujja]
A watan Yunin 2015, Rabinowitz ya kasance babban baƙo a fayafai na Desert Island na BBC Radio 4.
Rayuwa ta sirri
gyara sasheRabinowitz ya yi aure sau biyu. A ranar 15 ga watan Disamba 1944; matarsa ta farko ita ce Lorna Thurlow Anderson.[ana buƙatar hujja] Auren ya mutu a shekarar 2000.[ana buƙatar hujja]A watan Maris 2001, ya auri Maryamu (Mitzi) C. Scott.[ana buƙatar hujja]
Rabinowitz ya kai shekara 100 a ranar 26 ga watan Maris 2016. [2] Ya mutu ranar 22 ga Yuni 2016 a gidansa da ke a Lacoste, Vaucluse, Faransa. [3] Rabinowitz kafin mutuwarsa yana buga kidan piano a kowace rana a tsawon rayuwarsa har izuwa mutuwarsa. [4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Colin Larkin (writer). Missing or empty
|title=
(help) - ↑ "Harry Rabinowitz – Chariots of Fire, The Remains of the Day, The English Patient, The Talented Mr Ripley – is 100 today". Classical Source. 2016-03-26. Archived from the original on 2016-04-09. Retrieved 2016-03-30.
- ↑ "Bulletin municipal – Été 2016" (PDF). Lacoste municipality. Summer 2016. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "Harry Rabinowitz, TV and film composer and conductor, dies aged 100". Classicfm.com. Archived from the original on 27 September 2020. Retrieved 27 October 2019.
Karin madogarar bincike
gyara sashe- Debrett's People of Today. Debrett's Peerage Ltd, 2008.
- Marquis Who's Who, 2008.
- Strauss, Neil, "Lush Odes to the Art of Two Film Makers", in The New York Times, 19 September 1996, p. C16.