Hani Sewilam wani masanin ilimi ne ɗan ƙasar Masar kuma farfesa a fannin albarkatun ruwa a halin yanzu yana matsayin ministan ban ruwa. An zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar ministocin ruwa na Afirka a shekara ta 2023 na tsawon shekaru biyu.[1] Ya kasance shugaban Cibiyar Heribert Nacken kuma Darakta na UNESCO Shugaban Canje-canje na Ruwa da Gudanar da Albarkatun Ruwa da ke Jami'ar RWTH Aachen, Jamus.[2]

Hani Sewilam
Minister of Water Resources and Irrigation (en) Fassara

13 ga Augusta, 2022 -
Mohamed Abdel-Aaty (en) Fassara
Rayuwa
Karatu
Makaranta RWTH Aachen University (en) Fassara
(1 ga Afirilu, 1998 - 10 Oktoba 2002) Doctor of Philosophy (en) Fassara
Sana'a
Sana'a researcher (en) Fassara da ɗan siyasa
Employers The National Water Research Center (en) Fassara  (1 Oktoba 1991 -  30 Satumba 1997)
RWTH Aachen University (en) Fassara  (1 ga Afirilu, 1998 -  30 Satumba 2002)
RWTH Aachen University (en) Fassara  (1 Oktoba 2002 -  31 Mayu 2009)
Jami'ar Amurka a Alkahira  (1 Satumba 2011 -  31 Disamba 2012)
RWTH Aachen University (en) Fassara  (1 Satumba 2011 -

Ilimi da aiki

gyara sashe

Sewilam ya yi karatun Difloma a fannin Injiniyancin Ruwa da Digiri na farko a Injiniyanci da Ruwa a Jami'ar Zagazig, Masar. Daga nan ya wuce Jami'ar Southampton ta ƙasar Ingila inda ya sami digiri na biyu (MSc) a fannin injiniyan muhalli da ban ruwa da kuma digiri na uku a fannin sarrafa albarkatun ruwa daga jami'ar Aachen da ke Jamus.[3] Sha'awar karatunsa ta mayar da hankali kan kula da ruwa, ilimin ruwa, daskarewa da ci gaba mai ɗorewa.

Sewilam ya kasance manajan darakta na Unesco Chair a Canje-canje na Ruwa da Gudanar da Albarkatun Ruwa a Jami'ar RWTH Aachen, Bajamushe kuma daraktan ilimi na Sashen Injiniyancin Hydrology na Cibiyar Heribert Nacken. Sewilan shine shugaban Cibiyar Nazarin Aiwatarwa akan Muhalli da Ɗorewa (CARES) a Jami'ar Amurka a Alkahira (AUC).[4]

An naɗa shi Ministan Ruwa na Masar a ranar 13 ga watan Agusta 2022. A ranar 27 ga watan Fabrairu, 2023, Majalisar Ministocin Afirka kan Ruwa ta zaɓi Sewilam a matsayin shugaban kungiyar na tsawon shekaru biyu. Ya karɓi muƙamin Carl Hermann Schlettwein, ministan noma, ruwa da albarkatun ƙasa na Namibiya.[5]

An bashi lambar ta Ruwa-Makamashi-Abinci-Ecosystems (WEFE) Nexus a shekarar 2022.[6]

Manazarta

gyara sashe
  1. Nigeria, Guardian (2023-02-27). "Egypt's water resources minister, Sewilam becomes AMCOW president". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  2. "Appointment of apl. Prof. Hani Sewilam as Minister of Irrigation in Egyp... - RWTH AACHEN UNIVERSITY Faculty of Civil Engineering - English". www.fb3.rwth-aachen.de. Archived from the original on 2023-06-23. Retrieved 2023-06-23.
  3. "Egypt's irrigation minister heads to US for UN 2023 Water Conference - Society - Egypt". Ahram Online. Retrieved 2023-06-23.
  4. "Unilateral measures on Ethiopian dam pose 'existential danger' on 150M citizens: Egypt". EgyptToday. 2023-03-23. Retrieved 2023-06-23.
  5. "Message from the AMCOW President – African Ministers' Council on Water (AMCOW)" (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  6. Hassan, Nouran (2022-11-23). "Egyptian Minister of Irrigation and Water Resources Hani Sewilam received the Water-Energy-Food-Ecosystems (WEFE) Nexus award 2022". Identity Magazine (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.