Mawlawi Hamdullah Mukhlis (مولوی حمد اللہ مخلص) memba ne na Taliban Afghanistan kuma kwamandan Kabul Corps daga 4 ga Oktoba 2021 zuwa 2 ga Nuwamba 2021. Maulvi Hamdullah wanda kuma aka fi sani da Maciyin Kabul saboda shi ne babban kwamandan sojojin Taliban na farko da ya shiga fadar shugaban kasar Afganistan a ranar faduwar Kabul babban birnin kasar a shekara ta 2021. Hotunan da ke cikin fadar shugaban kasar bayan kwace iko sun nuna Maulvi Hamdullah zaune a kan kujerar tsohon shugaban kasar Ashraf Ghani da Amurka ke marawa baya. Hamdullah Mukhlis mamba ne na kungiyar Haqqani kuma babban jami’in soji na musamman na Badri . An kashe shi a ranar 2 ga Nuwamba 2021 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani asibiti a birnin Kabul.

Hamdullah Mukhlis
Rayuwa
ƙasa Afghanistan
Mutuwa Kabul, 2 Nuwamba, 2021
Sana'a
Sana'a hafsa da Ulama'u
Aikin soja
Digiri commanding officer (en) Fassara
Ya faɗaci Fall of Kabul (2021) (en) Fassara
2021 Taliban offensive (en) Fassara

Hamdullah ya mutu a ranar 2 ga Nuwamba, 2021, a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani asibiti a Kabul . Hamdullah Mukhlis shine shugaban Taliban mafi girma da aka kashe tun bayan da Taliban ta karbe iko da Afganistan a watan Agustan wannan shekara.