Hajiya Maryam (Captain Garba) an haifeta a shekarar ta alif dubu daya da dari Tara da tamanin da biyu (1982) a karamar hukumar Zaria dake jihar Kaduna a Najeriya.

Farkon Rayuwa

gyara sashe

Hajiya Maryam an haifeta a garin Zariya a shekarar ta alif dubu daya da dari Tara da tamanin da biyu (1982). Ita ce 'ya ta farko a wurin mahaifinta tana da kanne biyar sannan ta.[1]

Ta fara karatu a makarantar firamare dake unguwar sarki (wato Sarki Primary School) daga shekara ta alif dubu daya da dari Tara da casa'in da (1992) ta gama a shekara ta dubu daya da dari Tara da casa'in da takwas (1998) daga nan ta tafi makarantar Sakandire ta mata dake Kaduna (wato GGSS Kaduna).[2]

Maryam ta Yi aiki da kamfanin sadarwa na MTN inda ta rike mukamin manaja na shiyar jihar Kaduna. Ta Kuma Yi aiki da kamfanin Samar da wutar lantarki na jihar Kano daga shekara ta dubu biyu da biyu (2002) zuwa shekara ta dubu biyu da biyar (2005).

Manazarta

gyara sashe