Ciwon gyambon ciki shine rarakewa a cikin rufin ciki, bangaren farko na kananan hanji, ko kuma wani lokacin a kasan makogwaro .[1] [2] Ulcer a cikin ciki ana kiransa da ciwon ciki, yayin da daya daga cikin kashi na farko na hanji shine ciwon gyambon ciki na hanji . [1] Mafi yawan alamun bayyanar Gyambon ciki da hanji shine farkawa da dare tare da ciwon ciki na sama, da ciwon ciki na sama wanda yake tafiya idan mutum yaci Abinci abinci. [3] Tare da gyambon ciki, ciwon zai iya tsananta idan yakasance gyambon cikine na tumbi. [4] Sau da yawa ana kwatanta ciwon a matsayin ciwo mai zafi/kuna ko rashin jin daɗi. [3] Sauran alamun sun hasa da belching, amai, rage nauyi, ko rashin son cin abinci. [3] Kusan kashi uku na tsofaffi ba su da alamun cutar. [3] Matsalolin da zata iya kawowa na iya hadawa da zub da jini, Rarakeawa da toshewar ciki . [5] Zubar da jini yana faruwa a kusan kashi 15% na lokuta.[5]

Gyambon Ciki
Wikimedia set index article (en) Fassara da Wikimedia disambiguation page (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na pathologic processes (en) Fassara
NCI Thesaurus ID (en) Fassara C3426
inda wasu ke samun gyambo

Abubuwan da suka fi kawo cutar sun hada da kwayar cuta ta Helicobacter pylori da Magungunan kashe zafin jiki (NSAIDs).[6] Sauran, kananan abubuwan da ba a sani ba sun hada da shan taba, damuwa a sakamakon wasu yanayi mai tsanani na kiwon lafiya, cutar Behcet, cutar Zollinger-Ellison, cutar Crohn, da ciwon hanta.[6] [7]Tsofaffi sun fi zama cikin hadari da illolin ulcer wanda magungunan kashe ciwon jiki ke sakawa [8]. Anayin binciken gane cuatr ne gwalgwadon alamomin da mutum yazo dasu da kuma yin bincike na endoscopy ko barium swallow .[8] Ana iya ganokwayar cutar H. pylori ta hanyar gwajin jini. gwajin numfashi na urea, gwada bahaya don alamun kwayoyin cuta, ko gwajin gyambon ciki na biopsy.[8] Sauran yanayin da ke haifar da irin wannan alamun sun hada da ciwon daji na ciki, cututtukan zuciya, da kumburin rufin ciki ko kumburin gallbladder.[9]

Abincin ba ya taka muhimmiyar rawa wajen haifar ko hana gyambon ciki. [10] Ingattacen maganin ta ya hada da dakatar da shan taba, dakatar da amfani da magungunan kashe zafi na (NSAIDs), barin shan giya, da shan magunguna don rage yawan acid na ciki. [11] Maganin da ake amfani da shi don rage acid yawanci sun hada da mai hanawa na proton pump (PPI) ko mai hana H2, tare da shawarar farko ta jiya na sati hudu.[11] Gyambon ciki dalilin kwayar cutar H. pylori ana maganinta da hadin magunguna masu kashe kwayoyin cuta , irin su amoxicillin, clarithromycin, da PPI. [12] Rashi magani na kwayoyin cutar yanata karuwa kuma don haka magani bazai kasance koyaushe yana da tasiri ba. [13] Za a iyin maganin zaubar jini ta hanyar endoscopy, tare da bude tiyata yawanci ana amfani da su kawai a cikin yanayin da ba a yi nasara ba.

[14]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Empty citation (help)
  2. Empty citation (help)
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Empty citation (help)
  4. Empty citation (help)
  5. 5.0 5.1 Empty citation (help)
  6. 6.0 6.1 Empty citation (help)
  7. Empty citation (help)
  8. 8.0 8.1 8.2 Empty citation (help)
  9. Empty citation (help)
  10. Empty citation (help)
  11. 11.0 11.1 Empty citation (help)
  12. Empty citation (help)
  13. Empty citation (help)
  14. Empty citation (help)