Gurū Nānak (15 Afrilu 1469 - 22 Satumba 1539; Gurmukhi : ਗੁਰੂ ਨਾਨਕ; pronunciation: [gʊɾuː naːnəkᵊ], furuci ), wanda kuma ake kira Bābā Nānak ('baba Nānak'), [1] shine wanda ya kafa addini Sikh kuma shine na farkon daga cikin Gurayen Sikh guda goma. Ana gudanar da bikin haihuwarsa a duniya a matsayin Guru Nanak Gurpurab a ranar Katak Pooranmashi ('cikakken watan Kattak '), watau watan Oktoba zuwa Nuwamba.

Guru Nanak
leader (en) Fassara

- Guru Angad Dev (en) Fassara
1. Sikh guru (en) Fassara

- Guru Angad Dev (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Nankana Sahib (en) Fassara, 15 ga Afirilu, 1469
Mutuwa Kartarpur (en) Fassara, 22 Satumba 1539
Ƴan uwa
Mahaifiya Mata Tripta
Abokiyar zama Mata Sulakhni (en) Fassara
Yara
Ahali Bebe Nanaki (en) Fassara
Karatu
Harsuna Harshen Punjab
Sana'a
Sana'a guru (en) Fassara
Imani
Addini Sikh

An ce Nanak ya yi tafiya mai nisa a Nahiyar Asiya yana koya wa mutane ilimin ik onkar ( ੴ 'daya daga cikin allolinsu' ), wanda ke zaune a cikin kowane daya daga cikin halittunsa kuma ya shine gaskiya na har abada. [2] Tare da wannan ra'ayi, zai kafa wani dandamali na ruhannai, zamantakewa, da siyasa na musamman bisa tsarin daidaito, ƙauna na 'yan'uwa, nagarta, da kyawawan hali. [3] [4] [5]

Guru Nanak

Ana amfani da kalmomin Nanak a a matsayin nau'i na waƙoƙi 974, ko shabda, a cikin nassi mai tsarki na addinin Sikh, Guru Granth Sahib, tare da wasu manyan addu'o'i sune Japji Sahib ( jap  ; ji da sahib ɗafi ne masu nuna girmamawa); Asa di Var ('ballad na fatan alheri'); da Sidh Gosht ('tattaunawa da Siddhas '). Yana da wani ɓangare na imani na mabiya addinin Sikh cewa ruhu mai tsarki na Nanak, allahntaka, da dokokin addini suna sauka akan kowane Guru na gaba guda tara a duk lokacin da ake sauke waliyanci a kansu.

Tarihin Rayuwa

gyara sashe
 
Gurdwara Janam Asthan a Nankana Sahib, Pakistan, na tunawa da wurin da aka yi imanin an haifi Nanak.
 
Guru Nanak

An haifi Nanak a ranar 15 ga watan Afrilu 1469 a kauyen Rāi Bhoi Kī Talvaṇḍī (yanzu Nankana Sahib, Punjab, Pakistan) a lardin Lahore na Daular Musulunci na Delhi, [6] [7] ko da yake bisa ga wata al'ada, an haife shi a cikin watan Indiya na bikin Kārtik ko Nuwamba, wanda aka sani da Kattak a Punjabi. [8]

Manazarta

gyara sashe
  1. Macauliffe 1909.
  2. Hayer 1988.
  3. Sidhu 2009.
  4. Khorana 1991.
  5. Prasoon 2007.
  6. Singh 2006.
  7. Grewal 1998.
  8. Gupta 1984.