Gundumar Anloga
Gundumar Anloga na ɗaya daga cikin gundumomi goma sha takwas 18 a Yankin Volta, Na kasar Ghana. Asali yana daga cikin gundumar Keta mafi girma a lokacin a ranar 10 ga watan Maris shekarar alif dari tara da tamanin da tara 1989, wanda aka ƙirƙira shi daga tsohuwar Majalisar Gundumar Anlo. Ko yaya a ranar 19 ga Fabrairun shekarar 2019, yankin yamma na gundumar ya rabu don ƙirƙirar Gundumar Anloga a matsayin ɗayan gundumomi shida da Gwamnatin Akufo-Addo ta buɗe,[1][2] don haka sauran ɓangaren an riƙe su a matsayin Gundumar Karamar Hukumar Keta. Majalisar gundumar tana cikin kudu maso gabas na Yankin Volta kuma tana da Anloga a matsayin babban birninta.
Gundumar Anloga | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | ||||
Yankuna na Ghana | Yankin Volta | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Tekun Guinea | ||||
Sun raba iyaka da |
Wurare masu yawa a Yankin
gyara sasheBabban gari a cikin gundumar shine babban birnin, Anloga. Wasu daga cikin kauyukan sun hada da Alakple, Kodzi, Dzita, Dewegodo, Dewenu, Srogboe, Whuti, Atito, Fiaxor, Deta, Genui, Benadzi, Azanu, Apklorfudzi, Tregui, Trekume, Bleamezado, Dosukorpe, Lividzi, Agortoe, Salo, Fiato,Kpɔɖui,Adzato, Tegbi, Nyikutor, Suipe, Dzita, Bomigo, Ƒuveme, Anyaŋui, Tunu, Akplowotorkor, and others.[3]
Mutane
gyara sasheBabban kabila a Gundumar Anloga su ne mutanen Ewe. Babban rukunin Ewe sune Anlo Ewe. Shugabansu kuma sarkinsu shine Awormefia na Anlo, Togbui Sri na III.[1]
Gudanarwa
gyara sasheGundumar tana zaune ne a Anloga. Shugaban gwamnatinta shine Hakimin Gundumar (DCE) wanda Shugaban Ghana ya nada. (DCE) na yanzu shine Seth Yormenu.[4]
Hanyoyin haɗin waje
gyara sashe- Yanar Gizo Archived 2021-09-18 at the Wayback Machine
- Gundumomin Ghana a Statoids.com
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "New Anloga District Inaugurated". voltaregion.gov.gh. Volta Regional Coordinating Council. Retrieved 21 July 2020.
- ↑ "Government to inaugurate six new districts today". ghanaweb.com. GhanaWeb. 19 February 2019. Archived from the original on 21 July 2020. Retrieved 21 July 2020.
- ↑ "Agavedzi residents call for support after tidal waves render 700 homeless - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-05-29.
- ↑ "Group wants Anlo DCE removed over alleged corruption". myjoyonline.com.gh. 18 September 2019. Retrieved 21 July 2020.