Gudisa Shentema (Amharic: ጉድsa ሸntema; an haife shi a ranar 19 ga watan Afrilu 1980 a Ambo) ɗan wasan tsere ne na Habasha wanda ya ƙware a tseren marathon.[1]

Gudisa Shentema
Rayuwa
Haihuwa 19 ga Yuni, 1980 (43 shekaru)
ƙasa Habasha
Sana'a
Sana'a marathon runner (en) Fassara
Athletics
Sport disciplines marathon (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Ya lashe lambar tagulla a gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2003 kuma ya kare a matsayi na goma sha uku a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2005. Ya kuma yi takara a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2007, amma bai gama tseren ba.

Mafi kyawun lokacin sa shine 2:07:34 hours, wanda aka samu a cikin watan Afrilu 2008 a Marathon na Paris. A cikin tseren Half marathon nasa mafi kyawun lokacinsa shine 1:02:23 hours, wanda ya samu a watan Satumba 2005 a Philadelphia.

Bayan da ya yi hutun shekara biyu daga tseren gudun fanfalaki, ya samu nasarar lashe gasar Marathon na farko na Haile Gebrselassie a Habasha. [2]

Nasarorin da aka samu gyara sashe

Shekara Gasa Wuri Matsayi Taron Bayanan kula
Representing Template:ETH
2003 All-Africa Games Abuja, Nigeria 3rd Marathon 2:27:39

Manazarta gyara sashe

  1. worldathletics.org worldathletics.org https://worldathletics.org › ethiopia Gudisa SHENTAMA | Profile
  2. Ethiopian double at inaugural Haile Gebrselassie Marathon. IAAF (2013-10-21). Retrieved on 2013-10-24.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe