Moussa Sandiana Kaba wanda aka fi sani da suna Grand P mawaƙin Guinea ne, kuma ɗan wasan kwaikwayo, sannan kuma ɗan siyasa.[1]

Grand P
Rayuwa
Cikakken suna Moussa Sandiana Kaba
Haihuwa 11 Oktoba 1990 (34 shekaru)
ƙasa Gine
Karatu
Harsuna Faransanci
Susu (en) Fassara
Yaren Maninka
Sana'a
Sana'a music artist (en) Fassara
Sunan mahaifi Grand P
Kayan kida murya

Farkon rayuwa

gyara sashe

An haife shi a ranar 13 ga watan Oktoba, na a shekarar alif 1990 a Sanguiana, Nabaya, Guinea. Grand P an haife shi ne a cikin dangi masu arziƙi kuma an haife shi da wata cuta mai saurin yaɗuwa da ake kira progeria, don haka ya fara tsufa tun yana ƙarami.[1]

Shahararsa

gyara sashe

Grand P sanannen mawaƙi ne a ƙasar Guinea, a zahiri, yana ɗaya daga ciki mashahuran masu fasaha a Guinea. Ya fuskanci ƙalubale na rashin lafiya marasa adadi a lokacin farkon aikinsa amma hakan bai hana shi ganin ya cimma burinsa ba.[2]

Grand P ya samu ɗaukaka matuƙa a shekarar 2019 bayan nuna wani wasan kwaikwayon sa mai suna Kerfalla Kanté a babban birnin Guinea wato Conakry.[2]

Wasan Ƙwaiƙwayo

gyara sashe

Bayan wasan kwaikwayon, Grand P ya zama abin mamaki a yanar gizo kuma waƙarsa ta bazu kamar wutar daji, daga Guinea zuwa Mali, zuwa Cote d’Ivoire da sauran ƙasashe masu Magana da harshen Faransanci.

Ya kuma kasance daga cikin tawagar da suka wakilci kuma suka goyi bayan Guinea a Alkahira a Kofin Ƙasashen Afirka wato (CAN).

Ya fitar da waƙa mai taken “Indépendance” a ranar 2 ga Oktoba 2020 don bikin ranar samun ‘yancin Guinea. A cikin 2020, Grand P ya ba da sanarwar cewa zai tsaya takara a zaɓen Shugaban ƙasa.[3]

Ya bayyana cewa zai kafa ƙungiyar siyasa da ake kira Amour Consideration et Unite–“Soyayya, Nuna Tunani, da Haɗin Kai”.[3]

Grand P ya ƙulla alƙawarin aure shekarar 2020 ga zan kaɗeɗiyar budurwar sa mai suna Eudoxie Yao kuma sun yi aure a shekarar 2021.[4]

Manazarta

gyara sashe