Sakatariyar Tarayya bene ne mai hawa 15 a Ikoyi, Legas.[1][2]

An gina benen ne a shekarar 1976 don ma'aikatan gwamnatin tarayyar Najeriya. Makasudin ginin ya tsaya a 1991 bayan da aka mayar da matsayin Legas a matsayin babban birnin Najeriya zuwa Abuja, FCT.

Tun a shekara ta 2006, ginin ta kasance a cikin takaddamar shari’a tsakanin gwamnatin jihar Legas da wani kamfanin kera kadarori (Resort International Limited) wanda ya samu nasara a shari'ar don cigaba da gudanar da ginin daga hannun gwamnatin tarayya.

Duk da cewa hukumar NAFDAC ta na amfani da wani bangare na ginin na wucin gadi ginin ya kasance a cikin wani wuri da aka watsar da shi a tsawon rayuwarsa.

Manazarta

gyara sashe
  1. Dayo Ayeyemi (June 14, 2022). "FG Has Lost N88bn Revenue To Abandoned Old Federal Secretariat Ikoyi In 27 Years'". Nigerian Tribune. Retrieved August 28, 2022.
  2. "Restore Lagos federal secretariat complex, Society of Engineers urges govt". The Punch. Retrieved August 28, 2022.