Georgina Toth (an Haife ta a ranar 10, ga watan Maris 1982) 'yar ƙasar Hungarian ce kuma haifaffiyar ƙasar Kamaru ce mai wasan jefa guduma (hammer thrower). Toth tana da shaidar 'yar ƙasa biyu a Hungary da kuma Kamaru, kuma ta yi takara a Kamaru a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2008.[1]

Georgina Toth
Rayuwa
Haihuwa Dunaújváros (en) Fassara, 10 ga Maris, 1982 (42 shekaru)
ƙasa Kameru
Karatu
Makaranta Northern Arizona University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Sport disciplines hammer throw (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Toth ta halarci Jami'ar Arewacin Arizona da ke Flagstaff, Arizona, inda ta yi fafatawa a ƙungiyar guje-guje da tsalle-tsalle ta mata, kuma ta kammala karatun digiri a cikin shekarar 2009 tare da digiri na farko a fannin sarrafa kasuwanci-kudi da tallatawa.[2]

A duniya, ta kare a matsayi na hudu a Gasar Cin Kofin Afirka na 16th 2008.[3] Toth ta rike kambun kasa ga Hungary da Kamaru a cikin weigh and throw 19.69 m (64 ft 7 in), da rikodin ƙasa na Kamaru a cikin jefa guduma tare da 67.42 m.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. Georgina Toth . IAAF. Retrieved on 2014-09-21.
  2. Georgina Tóth Archived September 24, 2013, at the Wayback Machine . Sports Reference. Retrieved on 2014-09-21.
  3. Lumberjacks in London Archived 2014-01-26 at the Wayback Machine. North Arizona University. Retrieved on 2014-09-21.
  4. "Georgina Toth" . Tilastopaja OY athlete database. Retrieved 20 September 2011.