Gasar Gwajin Fikira da Basira ta Kasa a Katsina (KNTHC)

Gasar Gwajin Fikira da Fasaha ta Katsina (KNTHC),wata gasa ce ta baje kolin basira da gwamnatin jihar Katsina, take shirya a duk karshen shekara.wanda cibiyar baje koli da kirkire-kirkire tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki daga bangarorin ilimi da masana'antu na jihar a karkashin gwamnatin Aminu Bello Masari take daukan nauyi.[1] Babban makasudin taron shi ne karfafa kirkire-kirkire da kuma kara kaimi ga matasa a jihar musamman ma a Najeriya baki daya.[2]

Gasar Gwajin Fikira da Basira ta Kasa a Katsina (KNTHC)
Katsina National Talent Hunt

An fara gudanar da gasar ta masu hazaka ta kasa ne a shekarar 2020 tare da kira ga masu ganin cewa suna da basira don shiga gasar a tsakanin jihar da kuma sauran jihohin Najeriya. Gasar ta ƙunshi nau'ikan nunin baiwa guda huɗu: Fasaha da ƙira/zane-zane, ƙirƙirar ababe da samfura, Fasahar bayanai da sadarwa.[3] Arch. Faisal Umar Rafindadi ne jagorar wannan shiri na kasa

Manazarta

gyara sashe
  1. Royal, David O. (2022-03-13). "Masari: Changing Katsina youths narratives through talent hunt". Vanguard News. Retrieved 2022-11-23.
  2. NNN (2022-02-13). "Katsina talent hunt winner to get Toyota SUV, N5m". NNN. Retrieved 2022-11-23.
  3. "katsina National Talent Hunt Grand Finale". Retrieved 2022-11-23.