Gardin Sarki (tsofaffin sunayen hukumar Forces Nationales d’Intervention et de Securité.(1997-2011)[1][2] and Garde Republicaine (1963-1997),[2] (Garde Nationale du Niger) hukumar jami'an tsaro ce daga Rundunar Tsaron Nijar ƙarƙashin gudanarwar ma'aikatar harkokin cikin gida. Kwamandan Gardin Sarki na ƙasa shine babban kwamandan ta.

Gardin Sarki
gendarmerie (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1963
Sunan hukuma Garde nationale du Niger, Forces nationales d'intervention et de sécurité da Garde républicaine
Gajeren suna GNN da FNIS
Ƙasa Nijar
Shafin yanar gizo garde-nationale.interieur.gouv.ne
Gardin Sarki

Tarihi gyara sashe

 
Gardin Sarki

Da farko an kirkiri Gardin Sarki a shekara ta 1963 a karkashin shugabancin shugaba Diori Hamani. An damka tsaro na shugaban kasa kan Gardin Sarki a lokacin shugaba Seyni Kountche.[1] Bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 1995 tsakanin Gwamnatin Nijar da Abzinawa yan aware na arewacin kasar, aka sakema Gandun Sarki suna zuwa "Forces Nationales d'Interventions and Securite (FNIS)". Bayan yarjejeniyar ne aka saka tsaofaffin yan tawayen cikin rundunar ta Gandun Sarki. Da hukumar na karkashin ma'aikatar tsaro ne yayin da daga baya kuma aka sake mayar da ita ma'aikatar harkokin cikin gida a shekarar 2003. A zamanin mulkin Tandja Mamadou ansamu cikakkiyar jituwa tsakanin gwamnatin da Tandja. Lamarin ya kauce ne bayan juyin mulkin da ya faru da gwamnatin Tandja a shekarar 2010.[1]

Manufa gyara sashe

Manufofin hukumar Gardin Sarki na kunshe a ginshikai na n°201-61 na 7 ga Oktoba, 2010 sune:[3]

  • Sanya idanu a tafiyar da gwambati
  • Kiyaye kula da al'umma da wanzar da bin doka da oda
  • Kare gine-ginen kasa, al'umma da dukiyoyin su
  • Hobbasa a lokacin tsaro na ujila
  • Gudanar da aiyuka kan dokoki a karkara
  • Samar da aiyukan girmamawa ga shugabanni
  • Samar da kariya ga makarantun gwamnati
  • Bada gudunmuwa wake aiwatar da tsaron kasa.
  • Samar da gudanarwa, tsare-tsare da sanya idanu kan gidaje kaso
  • Saka gudunmuwa ga aiyukan cigaban kasa (kamar,mutunta dan'adamtaka)
  • Bada gudunmuwa wajen wanzar da zaman lafiya ga kasashen waje
  • Kare Mahalli
  •  
    Gardin Sarki
    Samar da taimako ga hukumomin gudanarwa dana diflonasiyyar kasashen waje.

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 Historical Dictionary of Niger pp. 244
  2. 2.0 2.1 [1] Archived 2014-07-14 at the Wayback Machine Gouvernance du secteur de la sécurité en Afrique de l’Ouest: les défis à relever – Le Niger
  3. "Archived copy" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2014-07-14. Retrieved 2014-06-10.CS1 maint: archived copy as title (link) Garde nationale du Niger