Fit for 55 ƙunshin ne da Tarayyar Turai ta ƙera don rage hayaƙin iskar gas na Tarayyar Turai da kashi 55% nanda shekarar 2030. Hukumar Tarayyar yankin Turai ta gabatar da ƙunshin a watan Yulin shekarar 2021. Ƙarƙashin ingantaccen tsarin doka, tsare-tsaren na iya zama doka acikin shekarar 2022. Matakan sun haɗada ƙarin tallafi don sufuri mai tsafta, abubuwan sabuntawa, da jadawalin kuɗin fito da ake kira Tsarin Dai-daita Kan Iyakar Carbon akan hayaƙi don shigo da iskar carbon mai yawa daga ƙasashen da ba suda isassun matakan rage gurɓataccen iskar gas insu.[1] Tana bada shawarar tsawaita Tsarin Kasuwancin Haɓɓaka Iskar hayaƙin Tarayyar yankin Turai don jigilar kayayyaki da zafi. Idan aka kwatanta da yanayin net-zero daga Hukumar Makamashi ta Duniya, shirin ya ƙunshi ƙarin matakan don tabbatar da cewa makamashi ya kasance mai araha. Ƙungiyar kare muhalli ta GreenPeace ta soki ƙunshin da cewa bai dace da dakatar da ɗumamar yanayi, bada kuma lalata muhimman tsare-tsare na taimakon rayuwa saboda abin da akayi hasashen ya yi kadan. Kungiyar ta soki rabe-raben makamashin halittu a matsayin makamashin da ake iya sabuntawa da kuma sayar da motocin da ba su da hayaki nan da shekarar 2035.

Duba kuma

gyara sashe
  • Canjin yanayi a Turai #Manufofin Yanayi

Manazarta

gyara sashe
  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Politico