FESPACO babban bikin fina-finai ne na Afirka wanda ake gudanarwa a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso. An fara wannan biki a shekarar 1969 kuma ya zama cibiyar haɗin kai da haɓaka fasahar fina-finai na Afirka. Bikin yana faruwa duk bayan shekaru biyu (biennial) kuma yana jan hankalin masu shirya fina-finai, ‘yan wasan kwaikwayo, da masu kallo daga ko’ina cikin faɗin duniya.

Abubuwan da ake yi

gyara sashe

Haska finafinai A lokacin FESPACO, ana nuna fina-finai daga ƙasashen Afirka daban-daban, gami da waɗanda aka shirya cikin harsunan gida ko na duniya.

Taron Dandalin Fina-Finai

gyara sashe

Masana'antu da masana fina-finai suna gudanar da tarurruka don tattauna matsaloli, cigaba, da kuma dabarun haɓaka fina-finai a Afirka.

kyaututtuka

gyara sashe

Bikin yana bayar da lambar yabo mafi girma, wato Étalon de Yennenga (Zinaren Yennenga), wanda ake bai wa mafi kyawun fim na Afirka. Wannan lambar tana ɗaukar suna daga Yennenga, wata jaruma a tarihin Burkina Faso.

Manazarta

gyara sashe