Felix A. Chami
Felix A. Chami masani ne daga Tanzaniya . Farfesa ne a Jami'ar Dar es Salaam, yana mai da hankali kan ilimin kimiya na bakin teku na gabashin Afirka.[1] Dokta Chami ya gano, a tsibirin Mafia da Juani, kayayyakin tarihi da suka bayyana Gabashin Afirka a matsayin wani muhimmin abu a cinikin Tekun Indiya .[2] Chami ya sami digiri na farko a fannin ilimin zamantakewa daga Jami'ar Dar es Salaam a shekarar 1986, inda ya yi digiri na biyu a fannin ilmin dan Adam a Jami'ar Brown a shekarar 1988 sannan ya yi Ph.D. a fannin ilimin kimiya na kayan tarihi daga Jami'ar Uppsala a 1994.
Felix A. Chami | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 20 century |
ƙasa | Tanzaniya |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | anthropologist (en) da archaeologist (en) |
Employers | Jami'ar Dar es Salaam |
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.