Fatuma (fim)
Fatuma (kamar Hadithi za Kumekucha: Fatuma ), fim ɗin wasan kwaikwayo ne na Tanzaniya na shekarar 2018 wanda Jordan Riber ya ba da umarni kuma darakta da kansa tare da iyayensa suka shirya: John Riber da Louise Riber. Shine cikon fim dinsa na farko na Hadithi za Kumekucha:TNU. Fim ɗin ya fito da Beatrice Taisamo a matsayin jagora tare da Ayoub Bombwe da Cathryn Credo a matsayin jarumai masu taimaka ma shirin.
Fatuma (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2004 |
Asalin harshe | Moroccan Darija (en) |
Ƙasar asali | Moroko |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Jordan Riber |
'yan wasa | |
External links | |
Fim ɗin ya yi bayani ne kan kuncin rayuwar mace da ƴarta a karkara inda take fuskantar ƙalubale da dama yayin da namiji ya tsoma baki a rayuwar ‘yarta. An yi fim ɗin a yankin Arusha na Tanzaniya. Har ila yau fim ɗin ya yi tasiri a shirin rediyon 'Kumekucha' wanda aka watsa a Tanzaniya a cikin 2016 da 2017.[1]
Kyauta
gyara sasheFim ɗin ya samu yabo sosai gami da kyaututtuka da dama a bukukuwan fina-finai na duniya.[2] Fim ɗin ya lashe kyautuka huɗu a fanni na musamman na Fina-finan Swahili a bikin Fim na Zanzibar na 2018 don Mafi kyawun Hoto, Fitacciyar Jaruma, Mafi Darakta, da Mafi kyawun Cinematography. Jarumar Catherine Credo ta lashe kyautar mafi kyawun jarumai yayin da Jordan Riber ta lashe kyautar gwarzo Darakta.
Yan wasan shirin
gyara sashe- Beatrice Taisamo a matsayin Fatuma
- Ayoub Bombwe a matsayin Manyusi
- Cathryn Credo a matsayin Neema
Manazarta
gyara sashe- ↑ "New movie features Africa's everyday superheroes, women farmers". Africa Lead. Archived from the original on 22 October 2020. Retrieved 17 October 2020.
- ↑ "Fatuma: AWARDS & FESTIVALS". MUBI. Retrieved 17 October 2020.