Fataucin mutane a ƙasar Faransa
Fataucin mutane a ƙasar Faransa Ƙasar Faransa ta hana fataucin mutane da kuma yin jima'i don biyan wani abun amfani (karuwanci) a ƙarƙashin maƙala ta 20 da ta 225 na kundin tsarin mulkin ƙasar.[1][2] Wanda ya ba da izini da hukuncin da ya dace akan waɗanda aka kama da laifin yin fyaɗe. A cikin watan Janairu shekara ta 2009, gwamnatin faransa ta gyara dokar ta da ke yaƙi da fataucin mutane don haɗa haɗa wata doka da kuma bayani akan yadda ake tilasta wa mutane yin aikin da bazasu iya ba ta hanyar bautar dasu.Gwamnati ta bayar da rahoton cewa ta samu mutane 19 masu aikata laifukan fataucin a ƙarƙashin hukumar ƙasar mai yaƙi da safarar mutane a shekarar 2008, shekarar da ta gabata wadda aka samu bayanai, idan aka kwatanta da Shekarar 2007 wadda aka samu mutane 33 da laifukan fataucin mutane a Faransa. Gwamnatin ƙasar ba ta tanada wani matsakaicin hukunci ga waɗannan masu safarar mutane su 19 ba, amma ta ce mafi girman hukuncin da za'a yanke musushi ne ya kai shekaru bakwai (7) a gidan yari. Bugu da ƙari, gwamnatin ƙasar Faransa ta bayar da rahoton samun ƙarin wasu mutanen 26 waɗanda aka kama su da laifin safarar yara ƙanana da kuma tilasta musu yin kasuwanci, da yi musu fyaɗe. Sai dai gwamnatin ƙasar ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan gyara hali/gidan yari.Jami'an Faransa sun ci gaba da dogaro da yawa kan tanade-tanade na hana fasa- kwauri na kundin tsarin mulkin kasar don hukunta wadanda ake zargi da safarar ƴan'mata don maida su karuwai. Gwamnati ta bayar da rahoton tuhume-tuhume 523 a ƙarƙashin dokar ta da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma fataucin mutane a shekarar 2008; kusan kashi 16 cikin ɗari na ainihin waɗanda aka kama an samesu ne da laifin fataucin mutane. Gwamnatin Faransa ta yi nasarar tarwatsa gungun masu fataucin mutane kusan 40 a Faransa a shekarar 2009 tare da haɗin gwiwar tarwatsa hanyoyin sadarwa na ƙasa da ƙasa guda 14 tare da abokan hulɗar ƙasashen biyu ta hanyar ƙungiyoyin bincike na haɗin gwiwa da ke da nufin yin bincike da kuma gurfanar da su a kan iyakokin ƙasar.[3]
Fataucin mutane a ƙasar Faransa | |
---|---|
human trafficking by country or territory (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | safarar mutane |
Ƙasa | Faransa |
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Trafficking in Persons Report 2017: Tier Placements". www.state.gov (in Turanci). Archived from the original on 2017-06-28. Retrieved 2017-12-01.
- ↑ "France". Trafficking in Persons Report 2010. U.S. Department of State (June 14, 2010). This article incorporates text from this source, which is in the public domain.
- ↑ "code pénal, livre II, titre II, chapitre V, section 1bis: De la traite des êtres humains" (in Faransanci). legifrance. December 1, 2011. Retrieved January 12, 2012.