Fadma Abi (ta mutu 2 ga Oktoba 2020) likitan fiɗa ce kuma farfesa. An ɗauke ta a matsayin mace ta farko 'yar ƙasar Morocco da ta fara aikin tiyata wanda a al'adance maza suka mamaye ta qa Maroko.[1]

Fadma Abi
Rayuwa
Haihuwa Khenifra (en) Fassara
Mutuwa 2 Oktoba 2020
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Koronavirus 2019)
Karatu
Makaranta University of Montpellier (en) Fassara
Sana'a
Sana'a likitan fiɗa


Tarihin Rayuwa gyara sashe

Fadma ta fito daga wani ƙaramin gari a Khenifra a tsakiyar Maroko. Ta zauna a Midelt na ɗan lokaci kafin ta wuce Meknes don yin karatun firamare a Lalla Amina.[1][2]

Sana'a gyara sashe

Fadma ta koma ƙasar Faransa don kammala karatunta na gaba ba da jimawa ba bayan ta kammala karatunta na uku a ƙasar Morocco. A cikin watan Yuli 1981, ta sami digiri a Janaral Anatomy da Organogenesis daga Jami'ar Montpellier. Ta kuma samu takardar shaidar difloma da kuma kwararriya a fannin aikin tiyata na gaba ɗay.[2]

A shekarar 1982, ta samu wannan nasara da ba kasafai ta samu ba inda ta zama mace ta farko da ta taɓa zama likitar tiyata a ƙasar Maroko a lokacin da Marigayi Hassan II ya karrama ta a matsayin Likitan tiyata mace ta farko a ƙasar Maroko a wani taron biki.[1] Ta kuma yi nasarar kammala aikin tiyatar bugun zuciya na farko a cikin wannan shekarar bayan ta zama kwararriyar Likita. A watan Yuni 1989, ta sami takardar shaidar karatu a cikin duban dan tayi (ultrasound) daga Jami'ar Paris. Ta fara aikin koyarwa a matsayin farfesa a jami'a a Faculty of Medicine and Pharmacy na Rabat a shekara ta 1992.[3]

Ta kuma fara gabatar da laccoci a jami'o'i da dama, taron manema labarai a duniya ciki har da kungiyar tiyata ta Endoscopic ta Gabas ta Tsakiya a cikin shekara ta 2019. Ta yi aiki musamman a matsayin shugabar ƙungiyar tiyatar Endoscopic ta Bahar Rum da Gabas ta Tsakiya a cikin shekara ta 2019. A cikin 2018, ta kuma yi aiki a matsayin Shugabar Majalissar Maghrebian na 22nd Association of Surgery Moroccan.[4]

Ta kuma shahara wajen karfafawa da horar da matasa musamman mata a Maroko su zama kwararrun likitocin fiɗa a nan gaba.

Mutuwa gyara sashe

Abi ta yi fama da ciwon daji a shekarunta na baya. Ta mutu a ranar 2 ga watan Oktoba, 2020, daga rikice-rikice na COVID-19.[5][6]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 "Morocco's first female surgeon dies of coronavirus". KAWA (in Turanci). 2020-10-07. Retrieved 2021-01-15.
  2. 2.0 2.1 "Pr Fadma Abi, un emblème de la chirurgie marocaine s'en va sur la pointe des pieds". Maroc Diplomatique (in Faransanci). 2020-10-04. Retrieved 2021-01-15.
  3. "Décès de la première femme chirurgienne marocaine (PHOTO)". Le Site Info (in Faransanci). 2020-10-03. Archived from the original on 1 November 2020. Retrieved 2021-01-15.
  4. "Marokko – Tod der ersten Chirurgin des Landes nach COVID-19 Erkrankung". Maghreb-Post (in Jamusanci). 2020-10-03. Retrieved 2021-01-15.
  5. "Vidéo. Décès de la première femme chirurgienne marocaine des suites du coronavirus". fr.le360.ma. 2020-10-03. Retrieved 2021-01-15.
  6. Hatim, Yahia (2020-10-06). "Three Prominent Moroccan Doctors Die of COVID-19 in One Day". Morocco World News (in Turanci). Retrieved 2021-01-15.