Fadia Farhani
Fadia Farhani (An Haife shi ranar 5 ga watan Fabrairun 1996) ƙwararriyar ƴar wasan taekwondo ce kuma ƴar Tunisiya.
Fadia Farhani | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 5 ga Faburairu, 1996 (28 shekaru) |
ƙasa | Tunisiya |
Sana'a | |
Sana'a | taekwondo athlete (en) |
Mahalarcin
|
Ta ci lambar tagulla a matakin wasan finweight a gasar Taekwondo ta duniya ta shekarar 2013, bayan da Anastasia Valueva ta doke ta a wasan kusa da na ƙarshe. Nasarorin da ta samu a gasar Taekwondo ta Afirka sun haɗa da lambobin zinare a shekarar 2014 da 2016, da lambar tagulla a 2018.[1]
A gasar share fagen shiga gasar Taekwondo ta Afirka ta shekarar 2016 ta lashe ɗaya daga cikin lambobin tagulla a gasar mata -49 kg.