Enver İzmaylov
Enver İzmaylov ( Ukraine, Russian: Энвер Измайлов ) an haife shi (12 ga Yuni, 1955) ɗan kabilar Tatar ne na Crimean kuma mawakin jita na jazz wanda ke amfani da salon bugawa Jitan mai amfani da lantarki.
Enver İzmaylov | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Fergana (en) , 12 ga Yuni, 1955 (69 shekaru) |
ƙasa |
Kungiyar Sobiyet Ukraniya |
Karatu | |
Harsuna | Harshan Ukraniya |
Sana'a | |
Sana'a | jazz musician (en) , guitarist (en) da jazz guitarist (en) |
Kyaututtuka | |
Artistic movement | jazz (en) |
Kayan kida | Jita |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Enver İzmaylov a Fergana, Uzbek Soviet Socialist Republic, Tarayyar Soviet acikin dangin Tatar Crimean da aka kora a baya daga Crimea wanda daga bisani ya sake komowa a 1989.
Duk da cewa yana kada jita tun yana dan shekara goma sha biyar, ya karanci bassoon a Makarantar Kida ta Fergana kuma ya kammala a 1973. Ya kasance memba na ƙungiyar Sato har na tsawon shekaru takwas kuma ya fito a cikin albam din Efsane (1986) da kuma Give Your Love for a Friend in a Circle a (1987). Ya koma makaranta ya sami digiri a Jami'ar Tashkert, sannan ya fara sana'ar solo.[1]
Dabaru
gyara sasheİzmaylov yana kada jita ne ta hanyar kadata ta wuyan gitar lantarki da yatsansa kamar keyboard.[2][3] Salo iri daya daya da ta makadin jita na salon jazz Stanley Jordan.[1]
İzmaylov yana kiɗan gargajiya na Crimean Tatar, Baturke, Uzbek, Balkan, kiɗan gargajiya, da kuma jazz . Yawancin sassan wakokinsa ana haɗa su cikin salo na lokaci kamar 5/8, 7/8, 9/8, 11/8, 11/16, da 13/16 waɗanda suka zama ruwan dare a salon kiɗan Tatar na Crimean. Yana da jita mai wuya uku wanda ake kera masa na musamman a Kyiv. Yana amfani da sauti guda biyu marasa daidaituwa: (daga ƙanana zuwa manya) E, B, E, E, B, E da C, C, G, C, C, C.[2]
Iyali
gyara sashe'Yar Enver Leniye İzmaylova shahararriyar mawakiya ce a tsakanin mawakan Tatar Crimean. Ta na kida da salon gargajiya, jazz, da kiɗan pop a cikin wakokinta.
Wakokinshi
gyara sashe- A Ferghana Bazaar (Tutu, 1993)
- Art na Duo tare da Geoff Warren (Tutu, 1996)
- Labarin Gabas (Boheme, 1998)
- Minaret (Boheme, 1999)
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Harris, Craig. "Enver Izmailov". AllMusic. Retrieved 12 August 2017.
- ↑ 2.0 2.1 Prasad, Anil (1 July 2010). "Enver Izmaylov". Guitar Player. Retrieved 13 August 2017.
- ↑ Yanow, Scott (2013). The Great Jazz Guitarists. San Francisco: Backbeat. p. 220. ISBN 978-1-61713-023-6.