Doki wata dabbace mai ƙafafuwa huɗu (4), wacce take da girma da ƙarfi tana kuma da gashi, amma mara yawa. Doki na da bindi mai tsawo kuma yana da gudun gaske. Haka kuma ana hawan doki da kuma wasa da shi. Sai dai ba a cin naman doki [1][2] A ƙasa hoton wani doki da kuma ta macen doki wato (goɗiya) tana shayar da ɗanta.

Doki
Doki
goɗiya tana shayar da ɗanta nono.

.

Amfani gyara sashe

Doki yana da amfani a gurin yan adam, suna amfani da shi tin a zamanin da wajen tafiye-tafiye da wasanni da noma da yaki da kuma ban ruwa a gona. Sannan kuma ana sanya wa doki linzami da abin hawa domin mutum ya hau saman kansa ya yi tafiya, sannan ana amfani da su a filin yaƙi.

Tarihi gyara sashe

Tin asali ɗan adam yana hawa doki domin bukatun kansa.

Al'adu gyara sashe

A al'adar mutane suna amfani da doki a lokacin bukukuwa da kuma wasannin gargajiya irinsu; tseren doki da hawan sallah da hawan daba da kuma gasar sarrafa doki.

A wasanni gyara sashe

A yaki gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "An kama masu sayar da naman doki a zaman na shanu a Turai". bbc hausa. 16 July 2017. Retrieved 10 July 2021.
  2. Othman, Fatima (7 June 2019). "Aisha Suleiman: Musulmar da ke kwallon doki a Kaduna". bbc hausa. Retrieved 10 July 2021.