David Villa Sánchez ( Spanish pronunciation: [daˈβið ˈbiʎa santʃeθ] ; an haife ne a uku ga watan Disamba shekarai alif dari tara da tamanin da daya 1981) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Sipaniya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan gaba a qungiyar qwallonm kafa ta barcelona . Masu fafutuka na kallon Villa a matsayin daya daga cikin fitattun 'yan wasan gaba na zamaninsa, kuma daya daga cikin fitattun 'yan wasan Spain na kowane lokaci. A halin yanzu yana aiki a matsayin Mashawarcin Fasaha kuma Shugaban Ayyukan Kwallon Kafa na Duniya na kulob din Super League na Indiya Odisha FC .

David villa a wasan hamayya da qungiyar real Madrid
David Villa

Wanda ake yiwa lakabin suna da El Guaje ( Yaron a Asturian ) saboda sunan wasan kwallon kafa tare da yara da suka girme shi, Villa ya sami mummunan ciwoda rauni tin yana yaro amma ya sami damar fara aikinsa a cikin manyan yan wasan qwallan qafa na ƙwararru tare da Sporting de Gijón a qasar sipaniya a shekarai dubu biyu da daya 2001. . Ya kuma koma Real Zaragoza anan qasar tasu ta sipaniya bayan yanayi biyu, inda ya fara buga gasar La Liga a qasar sipaniya, kuma ya lashe kofin Copa del Rey da Supercopa de España . Ya koma qungiyar Valencia a shekara ta dubu biyu da biyar 2005 kan kudin canja wuri na Yuromiliyan sha biyu kacal kuma sun sake daukar wani kofin Copa del Rey . A lokacin yana da shekaru ashirin da takwas 28, Villa ya yi rajistar kwallaye 28 a raga kuma ya sami ƙaura zuwa Barcelona akan Yuro miliyan arba'in a shjekarai2010, inda ya lashe gasar La Liga tare da barcelona na farko da UEFA Champions League, kuma ya zira kwallaye a wasan karshe na 2011 . Ya bar kulob din a cikin 2013 bayan ya kammala canja wurin € 5.1 miliyan zuwa Atlético Madrid, inda ya lashe wani lakabin La Liga. Bayan kakar wasa guda a babban birnin Spain, Villa ya tashi ya koma sabuwar kungiyar MLS ta New York City, inda ya zama dan wasan da ya fi zira kwallaye a kungiyar kuma ya yi fice, inda ya lashe kyautar MLS MVP Award na mafi kyawun dan wasa a 2016. A cikin 2018, Villa ya sanar da tashi daga New York, don shiga Vissel Kobe a Japan.

David Villa

Villa ya buga wasansa na farko a qasar sipaniya a shekara ta dubu biyu da biyar 2005. Ya halarci manyan wasannin gasa guda hudu, kuma ya kasance babba memba na kungiyoyin qasar sipaniya da suka ci kofin yuro na shekarai dubu biyu da takwasUEFA Euro 2008 da gasar cin kofin duniya na shekarai dubu biyu da goma 2010 . Ya zira kwallaye uku a gasar cin kofin duniya shekarai dubu biyu da shidda 2006, shi ne wanda ya fi zura kwallaye a gasar Euro 2008, kuma ya samu kyautar takalmin Azurfa a gasar cin kofin duniya ta 2010. Abubuwan da ya nuna don Spain da Valencia sun gan shi a cikin FIFA FIFPro World11 na 2010. Ya zama dan wasa na farko dan kasar Sipaniya da ya taba cin kwallaye 50 a duniya kuma, bayan ya dawo a takaice a shekarar 2017, ya yi ritaya daga buga wa kasar wasa da kwallaye 59 a wasanni 98 da ya buga, wanda hakan ya sa ya zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a Spain da kuma kasar. wanda ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin duniya, da kwallaye tara.

 

Yarantaka da fara aiki

gyara sashe
 
David Villa

An haifi Villa a qasar sipaniya a garin Tuilla, ƙaramin Ikklesiya a Langreo, Asturias, yanki a arewacin qasar tasu a sipaniya, ɗan José Manuel Villa, mai hakar ma'adinai . Lokacin da Villa ke dan yaro yana da shekaru hudu, damarsa ta zama dan wasan kwallon kafa ta shiga cikin hadari lokacin da ya samu raunin karaya a kafarsa ta dama, amma ya samu cikakkiyar lafiya daga baya. Saboda raunin daya samu, shi da mahaifinsa sunyi yi aiki a kan ƙarfafa hagu kafar da Villa kyakkyawan ya zama ambidextrous . Ya tuna cewa mahaifinsa ya kasance yana goyon bayansa a kowane lokaci: “Ya kasance yana can yana jefa mini kwallaye a raga akai-akai, yana sa ni bugun ta da kafar hagu lokacin da dama na ke cikin filasta bayan karya ta, ina da shekaru hudu. Da kyar na iya tunawa wani zaman horo daya da mahaifina baya nan. Ban taɓa kasancewa ni kaɗai a filin wasan ƙwallon ƙafa ba."

 
David Villa

Villa ya yarda kuma yanaji a jikinsa cewa ya kusa daina wasan kwallon kafa tin yana dan shekarusha hudu 14 bayan da ya kara ruguzawa da mai horar dasu. Duk da haka, saboda kwarin gwiwar da iyayensa suka ba shi, ya dage wajen neman yaga ya cika burinsa, ganin cewa basirarsa tana ganan a qwallan qadfa za ta iya samar masa da abin rayuwa. "A wancan zamanin ni ba kowa ba ne, ba na samun ko sisin kwabo kuma bayan an sanya ni in zauna a benci duk lokacin da nake so in tafi in yin wasa da abokaina," in ji shi. "Amma mahaifina kullum yana bani goyon baya yana karfafaman yana taya ni murna har sai da sana'ata ta juya." [1] Ya ci gaba da fara wasan ƙwallon ƙafa a UP Langreo kuma lokacin da ya cika shekaru 17 ya shiga makarantar ƙwallon ƙafa ta Mareo.

Club career

gyara sashe
  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named thriller