Daniel Anwuli
Daniel Anwuli (an haife shi a ranar 2 ga watan Mayu a shekara ta 1997) ɗan wasan dara ne na Najeriya. FIDE ta ba shi title na Master International a shekara ta 2019.
Daniel Anwuli | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 2 Mayu 1997 (27 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | chess player (en) |
Daniel Anwuli ya lashe Gasar Chess na Yammacin Afirka na shekarar 2019.,[1] cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta Chess a shekara ta 2019,[2] inda Maxime Vachier-Lagrave ya doke shi a zagayen farko.[3] Shi ne zakaran wasan dara na Najeriya na shekarar 2020.[4]
Anwuli ya wakilci Najeriya a gasar Chess Olympiad karo na 42 a Baku, Azerbaijan a shekara ta 2016 da kuma gasar Chess Olympiad na 43, a Georgia a shekarar 2018.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Daniel Anwuli rating card at FIDE
- Daniel Anwuli games at 365Chess.com
- Daniel Anwuli player profile and games at Chessgames.com