Dalia Hernández
Dalia Hernández Armenta (an haifeta ranar 14 ga watan Agusta, 1985) ƴar wasan kwaikwayo ce, ta ƙasar Meziko, wadda aka haifa a Veracruz, Mexico.[1] An santa saboda irin rawar ganin da ta taka a cikin fim ɗin Apocalypto (2006),[2] da The Legend of the Maska (2014) da kuma, Miracle Underground (2016).
Dalia Hernández | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Veracruz (en) , 14 ga Augusta, 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Mexico |
Karatu | |
Makaranta | Universidad Veracruzana (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo da dan wasan kwaikwayon talabijin |
IMDb | nm2199664 |
A cikin shekarar 2007, ta lashe lambar yabo ta Imagen Award don mafi kyawun goyon bayan ƴar wasan kwaikwayo, duba da rawar da ta taka a fim ɗin Apocalypto.[3] Ya taka rawa a cikin jerin shirin TV masu dogon Zango; "Capadocia del 2008" a cikin kashi na "María Magdalena" inda ya fito a matsayin "Rosa". A cikin 2014 ta taka rawar "Nayeli" a cikin The Legend of the Maska kuma a matsayin "Patricia" a cikin fim ɗin Miracle Underground.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Dalia Hernandez". CINeol (in Sifaniyanci). Retrieved 21 January 2016.
- ↑ "Best Movies of 2006". Lassen County Times. 16 January 2007. Retrieved 21 January 2016.
- ↑ "'Ugly Betty' Wins at 22nd Imagen Awards". AP Online. 29 July 2007. Archived from the original on 20 February 2016. Retrieved 21 January 2016 – via HighBeam Research.