Comfort Ekpo
Comfort Ekpo, listen ⓘ (an haife ta a ranar 12 ga watan Nuwamba 1954) mataimakiyar shugabar jami'a ta Najeriya a Jami'ar Uyo.
Comfort Ekpo | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
2000 - 2006
1993 - 1999
1983 - 1991
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Jahar Uyo, 12 Nuwamba, 1954 (70 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | Malami da mataimakin shugaban jami'a |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Comfort Memfin Ekpo a Uyo a shekara ta 1954. Iyayenta sune Etim Udoh Isok da Nyong Sam Akpan. Ta yi aiki har ta fara a matsayin malamar makarantar Lahadi (Sunday School teacher) kuma ta yi aiki a matsayin mataimakiyar mai koyarwa a Jami'ar Cross River daga shekarun 1983 zuwa 1991.[1]
Ekpo ta zama mataimakiyar shugabar jami'ar Uyo ta huɗu sannan kuma ta zama mataimakiyar shugabar jami'a mata ce ta farko.[2] A watan Disamba 2015, an shirya ta tafi kamar yadda aka bayyana Farfesa Enefiok Essien a matsayin magajin ta. Sai dai ta rubutawa Ministan Ilimi, Adamu Adamu cewa ta buƙaci a jinkirta naɗa wanda zai gaje ta. Hakan ya faru ne saboda zarge-zargen cin zarafi da kuma jabu da ake zargin an yi game da Essien da ake tattaunawa a jaridu.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Professor (Mrs) Comfort Memfin Ekpo BLS, Ed. M.Ed. Ph.D." Universal Learning Solutions (in Turanci). Archived from the original on 2020-02-26. Retrieved 2020-05-02.
- ↑ Leading Women[permanent dead link], 2014, SunNewsOnline.com, Retrieved 8 February 2016
- ↑ UNIUYO VC asks education minister to suspend appointment of professor indicted for sexual assault, December 2015, Premium Times NG, Retrieved 8 February 2016