Claudine Afiavi Prudencio ta kasance 'yar siyasa ce daga ƙasar Benin. [1] Ita ce shugabar Cibiyar Mata ta Jamhuriyar Benin, [2] da aka naɗa a Majalisar Ministoci. Mai girma shugabar kungiyar ci gaban sabuwar Benin (UDBN), ta kasance mataimakiya da minista sau da yawa.

Daga watan Oktoba 2010 zuwa Yuni 2021, ta kasance shugabar UDBN.

Tsakanin shekarun 2010 zuwa 2011, Prudencio ta kasance ministar sana'a da yawon buɗe ido.

Tsakanin shekarun 2011 da 2015, Prudencio ta kasance memba na Majalisar Dokoki ta ƙasa (Benin), sakatariyar majalisa ta farko, kuma memba ta Majalisar Pan-African Parliament.

Tsakanin shekarun 2015 da 2019, Prudencio ta kasance memba ta majalisa, shugabar kwamitin ilimi, al'adu, aiki da zamantakewa, memba ta Majalisar Pan-African, kuma memba ta Majalisar Dokokin La Francophonie.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.libre-express.com/1086/benin-l-udbn-de-claudine-prudencio-change-de-nom-et-devient-renaissance-nationale
  2. https://leleaderinfobenin.bj/info-benin-institut-national-de-la-femme-claudine-prudencio-nommee/