Cinema Vox wani gidan wasan kwaikwayo ne tun a ƙarni na 20 a Casablanca, Maroko.[1][2] Marius Boyer ne ya tsara shi kuma an kammala shi a cikin shekarar 1935, ƙarƙashin Kariyar Faransa. Ana ɗaukar sa a daya daga cikin manyan gidajen wasan kwaikwayo na fina-finai a Afirka.[1][3]

Cinema Vox
Wuri
Constitutional monarchy (en) FassaraMoroko
Region of Morocco (en) FassaraCasablanca-Settat (en) Fassara
Prefecture of Morocco (en) FassaraCasablanca Prefecture (en) Fassara
BirniCasablanca
Coordinates 33°35′40″N 7°37′09″W / 33.59453°N 7.61906°W / 33.59453; -7.61906
Map
Contact
Address Place des Nations Unies, 20000 Casablanca da Place de France, Casablanca
See caption
Hoton iska na Cinema Vox, 1950.

Gine-gine

gyara sashe

Tana da baranda guda uku da aka tattara kuma tana da wurin zama ga ƴan kallo har guda 2,000. Har ila yau, tana da silin mai lanƙwasa, wanda zai ba masu sauraro damar jin daɗin sanyin maraice.[1][4] Ginin yana da siffa ta “cubic mass,” wanda yayi daidai da Ginin Magasins Paris-Maroc na gaba. [1] Gine-gine na Vox ya ci gaba da zama abin nuni ga gidajen sinima da aka gina bayan 'yancin kai.

Ya kasance a dandalin Louis Gentil, yanzu wani yanki ne na Dandalin Majalisar Ɗinkin Duniya.[1]

Daban-daban

gyara sashe

Nass El Ghiwane ya sami manyan kiɗe-kiɗe a Cinema Vox.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Cohen, Jean-Louis, author. (2002). Casablanca : colonial myths and architectural ventures. ISBN 1-58093-087-5. OCLC 49225856.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
  2. Mechanical Power (in Turanci). Whitehall Press. 1938.
  3. Mechanical Power (in Turanci). Whitehall Press. 1938.
  4. Mechanical Power (in Turanci). Whitehall Press. 1938.
  5. Simour, Lhoussain (2016-10-21). Larbi Batma, Nass el-Ghiwane and Postcolonial Music in Morocco (in Turanci). McFarland. ISBN 978-1-4766-2581-2.