Cibiyar Ramayana kungiya ce ta al'adu da ta ruhi da ke cikin Union Park, Mauritius. An kafa ta ne a cikin shekarar 2001 ta hanyar wani doka da aka zartar a Majalisar Dokokin Jamhuriyar Mauritius don haɓakawa da yada almara na Hindu Ramayana da dabi'un ruhaniya, zamantakewa da al'adu da ke gudana daga gare ta. [1][2] Kafin wannan, babu wata majalisar dokoki ta wata kasa da ta kafa wata doka ko kafa wata cibiya don yada kyawawan dabi'u na Ramayana.

Cibiyar Ramayana
Bayanai
Farawa 2001

An amince da dokar gaba ɗaya a ranar 22 ga watan Mayu, a shekarar 2001 kuma shugaban ƙasar ya ayyana shi a matsayin doka a ranar 14 ga watan Yuni, a shekarar 2001. An wallafa shi a cikin Jaridar Gwamnati mai lamba 64 a ranar 30 ga watan Yuni, a shekarar 2001.[3]

Shugaban Cibiyar Ramayana Pandit Rajendra Arun, masani na Ramayana kuma marubucin litattafai da dama kan halayen Ramayana. A cikin shekarar 2002, a ranar Tulsi Jayanti, harsashin ginin cibiyar Ramayana wanda Firayim Minista, Anerood Jugnauth ya aza. Daga baya kuma firaministan lokacin Dr. Navinchandra Ramgoolam ya kaddamar da ginin a hukumance a shekarar 2007. [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Ramayana Center in Mauritius" . Hinduism Today Magazine . August 15, 2002. Retrieved 2015-09-22.Empty citation (help)
  2. "Ramayana Centre" . Mauritius Times . Retrieved 2015-09-22.
  3. "The Ramayana Centre Act 2001" (PDF). Ministry of Arts and Culture, Government of Mauritius. Retrieved 2015-09-22.
  4. "Ramayana Centre" . International Ramayana Conference 2015 . Retrieved 2015-09-22.