Cibiyar Manyan Yan Kasa
Cibiyar Manyan Yan Kasa, (Turanci:Senior Citizen Centre) wata hukuma ce ta Najeriya a ƙarƙashin Ma'aikatar Agaji, Gudanar da Bala'i da Kula da Jama'a[1].
Cibiyar Manyan Yan Kasa | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | government agency (en) |
Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya amince da kafa cibiyar manyan mutane ta ƙasa kamar yadda sashe na 16(2) (d) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999 ya tanada. Wannan gyare-gyaren Kundin Tsarin Mulki ya sa ya zama wajibi ga duk jihohi don samar da isassun ayyuka na zamantakewa ga tsofaffi a cikin al'umma da kuma inganta rayuwar su a matsayin manyan 'yan ƙasa.
Mai ritaya Air Vice-Marshal MA Muhammad ya samu muƙamin shugaban hukumar ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.[2][3]
Dokta Emem Omokaro shi ne Darakta Janar na cibiyar, kuma a wata hira da ta yi da shi, ta bayyana cewa ana ci gaba da tsare-tsare na jawo tsofaffin ƴan ƙasa a cikin al’umma don bayar da tasu gudunmawar a harkokin tattalin arziki a yankunansu daban-daban.
An kafa wannan babbar cibiyar ƴan kyasa a ƙarƙashin ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da kula da bala’o’i da jin dadin jama’a wacce ta riƙe Hajiya Sadiya Farouq a matsayin minista.[4]
Ministar Hajia Sadiya Farouq ta bayyana hakan ne a yayin kaddamar da aikin a ranar 7 ga watan Yuni 2021 a cibiyar samar da albarkatun kasa ta Najeriya, Abuja cewa an amince da manufar tsufa don kare hakkin tsofaffi.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Osuji, Grace (2021-06-08). "FG Inaugurate Board Of National Senior Citizens Centre, Approves National Policy On Ageing". Federal Ministry of Information and Culture (in Turanci). Retrieved 2022-03-30.
- ↑ "FG inaugurates board for national senior citizens centre". TheCable (in Turanci). 2021-06-07. Retrieved 2022-03-30.
- ↑ "FG inaugurates board for national senior citizens centre". TheCable (in Turanci). 2021-06-07. Retrieved 2022-03-30.
- ↑ Admin. "Buhari establishes centre for Nigeria senior citizens". Premium Times.
- ↑ "FG inaugurates board for national senior citizens centre". TheCable (in Turanci). 2021-06-07. Retrieved 2022-03-30.