Christiane Brunner
Christiane Brunner (an haife ta ranar 23 ga watan Maris, 1947) a Geneva. 'yar siyasan Switzerland ce kuma lauya.
Christiane Brunner | |||||
---|---|---|---|---|---|
4 Disamba 1995 - 2 Disamba 2007
25 Nuwamba, 1991 - 3 Disamba 1995 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Geneva (en) , 23 ga Maris, 1947 (77 shekaru) | ||||
ƙasa | Switzerland | ||||
Karatu | |||||
Harsuna | Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa, Lauya da trade unionist (en) | ||||
Wurin aiki | Bern (en) | ||||
Kyaututtuka | |||||
Fafutuka |
Feminism trade unionism (en) | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Social Democratic Party of Switzerland (en) |
Aiki
gyara sasheBrunner ta mallaki mukamai masu zuwa:
- Mataimakin Babban Majalisar Canton na Geneva, 1981–1990
- Memba na Majalisar Kasa, 1991–1995
- Memba na Majalisr Jihohi, 1995–2007
- Shugaban Jam'iyyar Socialist na Swiss, 2000–2004
Siyasa
gyara sasheZaben 1993
gyara sasheBrunner ita ce 'yar takarar jam'iyyar Socialist lokacin da René Felber ya yi ritaya daga Majalisar Tarayya a 1993. A ranar 3 ga Maris 1993 Majalisar Tarayya ta zabi Francis Matthey, duk da haka ya bar wannan mukamin saboda adawar jam’iyyarsa. A ranar 10 Maris 1993 Ruth Dreifuss aka zaba a Majalisar Tarayya a kan Christiane Brunner.
Matsayi
gyara sasheBrunner tana da matukar aiki a cikin al'amuran da suka shafi kungiyoyin kwadago (ita ce shugabar kungiyar ta FTMH), kuma ta kasance memba na Majalisar da ta shiga tsakani lokacin da aka tattauna batutuwa irin su Tsaron Jama'a da dokokin aiki.
A halin yanzu ita ce shugabar Kwamitin Tsaron Jama'a da Lafiyar Jama'a a Majalisar Jihohi (CSSS-CE).