Cécile Ndjebet
Cécile Bibiane Ndjebet 'yar Kamaru ce mai fafutukar kare muhalli kuma mai kula da gandun daji. Ta shahara da ayyukanta na inganta yancin mata na filaye da dazuzzuka. Ita ce ta lashe kyautar Wangari Maathai a shekarar 2022. [1]
Cécile Ndjebet | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Cécile Bibiane Ndjebet |
ƙasa | Kameru |
Sana'a | |
Sana'a | agronomist (en) da forester (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Cécile Ndjebet a wani ƙauye kusa da Edea a yankin Littoral na Kamaru. Mahaifiyarta manoma ce. [2] Ta yi digirin digirgir a fannin gandun daji na zamantakewa daga Jami'ar Aikin Noma ta Wageningen da ke Netherlands. [3]
Sana'a
gyara sasheCecile Ndjebet ta fara jigilar ta a Kamaru a matsayin ma'aikaciyar gwamnati. A shekarar 2012, an zaɓe ta a matsayin shugabar canjin yanayi na hukumar kula da dazuzzuka ta Afirka ta tsakiya. [4] Ita ce shugabar kungiyar mata ta Afirka don kula da gandun daji (REFACOF), kungiyar da ke inganta shigar mata a fannin sarrafa albarkatun ƙasa a ƙasar Kamaru da ta kafa a shekarar 2001. [4]
A watan Nuwamba 2022, an ba ta lambar yabo ta UNEP's Champions of the Earth. [5]
Kyauta
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Woo-hyun, Shim (2022-05-08). "African activist Cecile Ndjebet wins 2022 Global Forest Championship Award". The Korea Herald (in Turanci). Retrieved 2023-04-30.
- ↑ "La Camerounaise Cécile Bibiane Njebet lauréate du prix Champions de la Terre de l'ONU". RFI (in Faransanci). 2022-11-23. Retrieved 2023-04-30.
- ↑ "Ms. Cécile Bibiane Ndjebet | Department of Economic and Social Affairs". sdgs.un.org. Retrieved 2023-04-30.
- ↑ 4.0 4.1 "Laureate pushes for women's rights and a greener future". UNEP (in Turanci). 2022-11-25. Retrieved 2023-04-30.
- ↑ Melody, Chironda (5 December 2022). "Cameroon: Cécile Bibiane Ndjebet - A Champion Who Pushes for Women's Land and Forest Rights #AfricaClimateHope". Allafrica. Retrieved 30 April 2023.
- ↑ "News: Cameroonian activist wins Wangari Maathai Forest Champions' Award 2022". Global Landscapes Forum (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
- ↑ Italia, UNRIC (2023-03-15). "UNEP's 2023 Champions of the Earth Award with a focus on plastic pollution solutions". ONU Italia (in Italiyanci). Retrieved 2023-05-01.