Bruno Lourenço Pinto de Almeida Paz (an haife shi a ranar 23 ga watan Afrilu 1998) ɗan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a kulob din Süper Lig Konyaspor a matsayin mai tsaron gida. An haife shi a Portugal, yana buga wa tawagar kasar Angola wasa.

Bruno Paz
Rayuwa
Cikakken suna Bruno Lourenço Pinto de Almeida Paz
Haihuwa Barreiro (en) Fassara, 23 ga Afirilu, 1998 (26 shekaru)
ƙasa Portugal
Harshen uwa Portuguese language
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Sporting CP B (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Tsayi 1.82 m

Aikin ƙwallon ƙafa gyara sashe

A ranar 6 ga watan Agusta 2016, Paz ya fara halarta na farko tare da Sporting B a wasan 2016-17 LigaPro da Portimonense.[1]

Paz ya fara buga wasansa na farko a kulobɗin Sporting CP a watan Disamba 2018, lokacin da ya kasance mai maye gurbin na mintina 73 a wasan da ci 3-0 na gasar Europa da Vorskla Poltava.[2] [3]

 
Bruno Paz

A ranar 23 ga watan Mayu 2022, Paz ya sanya hannu kan kwangilar shekaru biyu (tare da zaɓin tsawaita shekara ɗaya) tare da kulob ɗin Konyaspor a Turkiyya.[4]

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

 
Bruno Paz

An haifi Paz a Portugal iyayensa 'yan Angola ne. Shi matashi ne na kasa-da-kasa na Portugal, wanda ya buga wasa har zuwa Portugal U20s. An kira shi zuwa tawagar kasar Angola don buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na 2023 a watan Maris 2023.[5]

Manazarta gyara sashe

  1. "Sporting B 1-2 Portimonense" . ForaDeJogo. 2016-08-06. Retrieved 2016-08-09.
  2. "The lowdown on 3m euro-rated midfielder linked with Reds" . 2 June 2020.
  3. "Sporting Lisbon vs. Vorskla - 13 December 2018 - Soccerway" .
  4. "Bruno Paz İttifak Holding Konyaspor'umuzda" [Bruno Paz is at Konyaspor] (in Turkish). Konyaspor. 23 May 2022. Retrieved 19 October 2022.
  5. "Pedro Soares Gonçalves convence Bruno Paz a atuar por Angola" . www.record.pt .

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe