Brother Jed
George Edward "Jed " Smock, Jr. (an haife shi a Janairu 4, 1943 - 6 ga Yuni, 2022), wanda aka fi sani da Brother Jed, wani Ba'amurke ne mai wa'azin bishara,wanda yake wa'azi a gaban jama'a a kolejoji. Ya yi wa’azi a kwalejoji a duk jihohin Amurka hamsin, da kuma a wasu ƙasashe. [1] A matsayinsa na mai wa'azin tafiya, yawanci yakan ɗauki 'yan kwanaki ne a kowane harabar, yana zuwa makarantun arewa a damina da bazara da kuma yankuna kudu a watannin hunturu. A cikin 2004 ya koma Columbia, Missouri inda yake yawan yin wa'azi a Jami'ar Missouri da sauran kwalejoji a kusa da Yamma ta Tsakiya. A lokacin rani na 2013 ya ƙaura da hidimarsa da gidansa zuwa garinsa na Terre Haute, Indiana .
Brother Jed | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Brookings (en) , 4 ga Janairu, 1943 |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mutuwa | 6 ga Yuni, 2022 |
Karatu | |
Makaranta | Indiana State University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai da'awa da Mai da'awa |
Imani | |
Addini |
United Methodist Church (en) Evangelicalism (en) |
IMDb | nm3818977 |
brojed.org |