Boma Iyaye
Boma Iyaye (an haife shi ranar 24 ga watan Satumban 1969) Akanta ne na Jihar Ribas, ɗan siyasa kuma Kwamishinan Wasanni.[1]
Boma Iyaye | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Shekarun haihuwa | 24 Satumba 1969 |
Sana'a | civil servant (en) |
Ilimi a | Jami'ar jihar Riba s da Baptist High School (en) |
Ɗan bangaren siyasa | Rivers State People's Democratic Party (en) |
Ilimi
gyara sasheYa yi karatu a State School II Port Harcourt tsakanin shekarar 1974 zuwa 1980. Ya halarci makarantar sakandare ta Baptist don karatun sakandare daga shekarar 1981 zuwa 1986. Bayan shekara guda, ya shiga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas kuma ya karanta Accountancy. Daga nan ya kammala shirin aikin bautar ƙasa na wajibi na shekara ɗaya.[2]
Sana'a
gyara sasheIyaye ya fara aikinsa a kamfanoni masu zaman kansu a matsayin akawu. Ya yi aiki tare da kamfanoni da yawa tsakanin shekara ta 1992 da 2003. Daga baya ya shiga harkokin siyasa kuma ya samu nasarar tsayawa takarar kujerar majalisar dokokin jihar Ribas, inda ya yi aiki har zuwa 2007 yana wakiltar Ogu – Bolo. Ya kasance shugaban kwamitin majalisar kan harkokin wasanni da kuma mamba na sauran kwamitoci a majalisar.[2]
A cikin watan Disamban 2015, an shigar da shi cikin Majalisar Zartarwa ta Wike a matsayin Kwamishinan Wasanni. Iyaye ya taɓa yin aiki a wannan ofishi daga ranar 4 ga watan Afrilun 2008 zuwa ranar 4 ga watan Yunin 2009, da kuma daga Yulin 2009 zuwa Yunin 2011.[2]
A ranar 28 ga watan Disamban 2021, an naɗa mai girma kwamishinan a matsayin shugaban rukunin gidaje na Chiri War Canoe House of Loko a masarautar Ogu ta ƙaramar hukumar Ogu-Bolo ta jihar Ribas.[ana buƙatar hujja]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "The Rivers State Commissioner Sports, Boma Iyaye has Constituted a six-man committee to re-organize the two State-owned professional football clubs, Sharks and Dolphins". Today FM. 19 January 2016. Retrieved 21 September 2016.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 https://web.archive.org/web/20130806083742/http://riversstate.gov.ng/government/a-z-list-of-mda-s/414-sports-ministry.html