Antony John Blinken (an haifeshi 16 ga watan Afrilu, 1962) ma'aikacin gwamnatin Amurka ne kuma dan diflomasiyya ne wanda yake aiki tun 26 ga watan Janairu, 2021 a matsayin sakataran Amurka na 71. Yayi aiki a matsayin mataimakin mai bada shawara a kan tsaro na kasa daga 2013 zuwa 2015 da kuma mataimakin sakataran kasa na kasar Amurka daga 2015 zuwa 2017 a karkashin gwamnatin shugaba Barack Obama.

Blinken antony j. blinken ministar harkokin wajen Amurka
Blinken antony j. blinken

Tarihi da kuma karatu

gyara sashe

An haife Blinken a 16 ga watan Afrilu a shekarar 1962, a Yonkers dake jahar New York, iyayenshi Yahudawa ne, Judith (Frehm) da Donald M. Blinken, wanda yayi aiki a matsayin ambasadan Amurka a kasar Hungari. kakanninshi na bangaren uwa Yahudawa ne na kasar Hungari. Kawun Blinken, Alan Blinken yayi aiki a matasayin ambasada na Amurka a kasar Beljiyan. Kakanshi na bangaren uba, Maurice Henry Blinken yana daga cikin magoya bayan Isra'ila na farko-farko wanda ya karanci tattalin arzikinta, kuma kakan kakanshi shine Meir Blinken, marubuci ne na yaren Yiddish.

Blinken yayi karatu a makarantar Dalton dake cikin birnin jahar New York har zuwa 1971. Blinken yayi karatu a jami'ar Harvard daga 1980 zuwa 1980 inda yayi karatu a kan zamantakewa.

Manazarta

gyara sashe