Bintou
Bintou (wanda kuma aka sani da A Close-Up on Bintou ) ɗan gajeren fim ne da akayi shi a shekarar 2001 na ƙasar Burkinabé wanda Fanta Régina Nacro ya ba da umarni. Ya zama wani ɓangare na 2002 Collection Mama Africa.
Bintou | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2001 |
Asalin harshe | Mooré |
Characteristics | |
Direction and screenplay | |
Darekta | Fanta Régina Nacro (en) |
External links | |
Specialized websites
|
Labarin fim
gyara sasheBintou, Uwar ’ya’ya uku ce maigidanta Habila, ya yi masa dukan tsiya, saboda ta yi amfani da kuɗin aikin gida wajen biyan ɗiyarta makaranta domin ta samu ilimin da aka hana ta tun kuruciyarta. Ya yi imanin cewa 'ya'yansa ne kawai ya kamata su yi karatu. Tun da mijinta ya ki biyan ɗiyarta ta karatu, Bintou ta kuduri aniyar samun kuɗin da kanta, duk da haka, fasaha daya da take da ita ita ce noman gero. Dole ne ta nemo tukwane, kuma ta sami buhunan gero daga ma'ajiyar, yayin da mijinta ya ci gaba da yi mata zagon kasa.[1][2]
'Yan wasa
gyara sashe- Hyppolite Ouangrawa a matsayin Habila, mijin Bintou
- Alima Salouka a matsayin Bintou
Kyautattuka
gyara sasheBintou ta lashe lambobin yabo da yawa a cikin shekarun 2001 da 2002 ciki har da a Cannes Film Festival, Amiens International Film Festival, Bermuda International Film Festival, Clermont-Ferrand International Short Film Festival, Marrakech International Film Festival da Ouagadougou Panafrican Film and Television Festival.[1][3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedFRN
- ↑ "Mama Africa" (PDF). BFI. 2005-07-21. Retrieved 2008-02-09.[permanent dead link]
- ↑ "Awards for Bintou". Internet Movie Database. Retrieved 2007-12-29.