Hajiya Binta Kofar Soro ko Hajiya Binta a takaice, kamar yanda abokan sana’arta na Kannywood ke yawan kiranta. (An haife ta a ranar 24 ga watan Nuwamba shekara ta alif dari tara da saba'in 1970, ta rasu a ranar 4 ga watan mayu shekara ta alif dubu biyu da sha Tara 2019), a cikin kwaryar birnin Katsina. Fitacciyar Jaruma ce a masana’antar kannywood.

Farkon Rayuwa da Ilimi

gyara sashe

Ta yi karatunta na allo da boko duk a garin Katsina kamin ta yi aurenta na farko.

Aikin Fim

gyara sashe

Fitacciyar jarumar tana yawan fitowa a matsayin uwa a Faifayen shirin Kannywood matsayin da ya wuce gaban wasan kwaikwayo, har a zahiri yan wasan suna ɗaukarta tamkar uwa a garesu saboda rikon gaskiya, tausayi, shawarar da take basu kamar ita ta haifesu. Hajiya yar siyasace ta sahun gaba wadda take gwagwarmayar kwato ma tallakawan yankinta yancinsu da ake danne masu, yar kasuwace ita, sannan sai sana’ar da munka santa da ita wato wasan kwaikwayo wadda a cikinta ta yi fice wanda shike. Tana daukar matsayin uwa a faifayen shirin da take fitowa kamar irinsu Hajara Usman, wani lokacin ta fito matsayi irin na su Saratu Daso wato Muguwa ko Mayya.

Hajiya Binta tana daga cikin 'yan wasan kwaikwayo yan asalin Jahar Katsina da ke haskaka akwatunan kallon masu kallo.

GobirMob na taya daukacin Masana’antar Kannywood da Katsina jimamin mutuwar Hajiya Binta Kofa Soro.[1]

Rasuwar ta

gyara sashe

Hajiya Binta kofar soro Allah yayi mata rasuwa ranar asabar, wacce tayi daidai da 4 ga watan mayu shekara ta 2019, a gidanta da ke unguwar Fillin Samji dake cikin kwaryar birnin katsina.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-01-28. Retrieved 2020-11-12.
  2. https://www.bbc.com/hausa/labarai-48170411