Bin doka kafin kafa doka
Bin doka kafin tabbatar da doka, wanda kuma aka sani da daidaito a ƙarƙashin doka, daidaito a gaban shari'a, daidaiton shari'a, ko daidaiton doka, shi ne ƙa'idar cewa dole ne a ba da kariya ga kowa da kowa ta hanyar bin doka.[1] Ƙa'idar tana buƙatar tsari mai kyau na doka wanda ke bin tsarin da ya dace don samar da adalci da daidaito akan kowa, kuma yana buƙatar kariya daidai gwargwado don tabbatar da cewa babu wani mutum ko rukuni na mutane da za su sami gata/fifiko akan wasu ta hanyar karya doka.Wani lokaci ana kiran ka'idar Isonomy tana tasowa daga tambayoyi daban-daban na falsafa game da daidaito da kuma adalci akan kowa ba tare da nuna wariya ba .Daidaito kafin tabbatar da doka yana ɗaya daga cikin mahimman ƙa'idojin masu nuni da ma'anar ƴanci. Bai dace a bautar da shari'a ba,
Don haka dole ne a yi wa kowa adalci a karkashin doka ba tare da la'akari da launin fata, jinsi, launi, kabila, addini, nakasa, ko wasu halaye ba, ba tare da wani gata/fifiko, wariya ko bangaranci ba. Babban garantin daidaito kafin tabbatar da doka yana samuwa ta mafi yawan kundin tsarin mulki na duniya, amma takamaiman aiwatar da wannan garantin ya bambanta a ƙasashen duniya.Misali, yayin da yawancin kundin tsarin mulki ke tabbatar da daidaito ba tare da la’akari da launin fata ba, kaɗan ne kawai ke ambaton ƴancin yin daidaito ba tare da la’akari da ɗan ƙasa ba ko wanda ba ɗan ƙasa ba, misali a lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin ƙasar Ukraniya da Rasha a yayin da mutane ke neman mafaka da yawa daga cikin baƙaƙen fata sunce ana nuna banbanci wajen taimako da kuma wajen bawan abin hawa.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Universal Declaration of Human Rights". www.un.org. Retrieved 7 March 2022.
- ↑ "Read about "Equality" on Constitute". constituteproject.org. Retrieved 7 March 2022.