Bikin Adikanfo biki ne na shekara-shekara wanda sarakuna da mutanen Hwidiem a yankin Ahafo, a da yankin Brong Ahafo na Ghana ke yi.[1] Akan yi bikin ne a watan Satumba[2]. Wasu kuma suna da’awar ana yin ta ne a cikin watannin Maris ko Afrilu.[3]

Infotaula d'esdevenimentBikin Adikanfo
Iri biki
Wuri Hwidiem, Yankin Ahafo
Ƙasa Ghana

A lokacin bikin, ana maraba baƙi don raba abinci da abin sha. Mutanen sun sanya kayan gargajiya kuma akwai durbar na sarakuna. Akwai kuma raye-raye da buge-buge.[4] Ana yin hadayun dabbobi ga gumakansu da kakanninsu.[3]

Muhimmanci

gyara sashe

Ana gudanar da wannan biki ne domin nuna wani lamari da ya faru a baya.[5] Wannan biki na tunawa da hijirar mutanen Hwidiem daga Denkyira Ntomu zuwa mazauninsu na yanzu.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "GSB - Hwidiem State Book". ghanastatebook.com. Retrieved 2020-08-24.
  2. "Festivals Ghana - Easy Track Ghana". www.easytrackghana.com. Retrieved 2020-08-24.
  3. 3.0 3.1 3.2 "National Commission on Culture - Ghana - Brong Ahafo Region". www.s158663955.websitehome.co.uk. Retrieved 2020-08-24.
  4. "Major Festivals". www.ghanaembassyiran.com. Retrieved 2020-08-21.
  5. "The Consulate General Of The Republic of GHANA in The United Arab Emirates (Dubai)". www.ghanaconsulatedubai.com. Archived from the original on 2020-08-15. Retrieved 2020-08-21.