Bibata Ouédraogo 'yar Burkinabe ce, mai fafutukar kare hakkin mata kuma tsohuwar malamar makaranta. [1]

Bibata Ouédraogo
Rayuwa
ƙasa Burkina Faso
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a Mai kare hakkin mata, gwagwarmaya da mai karantarwa

Ta shahara da kokarinta na inganta hakokin jima'i da haihuwa da kuma hakkin kula da lafiyar mata masu juna biyu a Burkina Faso. [2] Ta kuma gudanar da bincike da wayar da kan jama'a game da yaki da cutar kanjamau, kuma ta kasance mai fafutukar yaki da wariyar jinsi da auren ƙananan yara. [3] [4]

A halin yanzu tana riƙe da muƙamin shugabar kungiyar AFDEB reshen Ouahigouya wacce kungiya ce ta mata don ci gaban Burkina Faso. Ta kuma yi aiki a matsayin malama kuma ta yi ritaya daga koyarwa a shekarar 2013. [5] Ta ci gaba da kokarinta na jin kai da fafutuka ko da bayan ta yi ritaya daga koyarwa.


A watan Agusta 2021, an sanya ta a matsayin ɗaya daga cikin mata bakwai masu fafutuka na Afirka waɗanda suka cancanci muƙalar Wikipedia ta Global Citizen, ƙungiyar ƙasa da ƙasa da ƙungiyar bayar da shawarwari. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "My Body My Rights Burkina Faso". www.amnesty.org (in Turanci). Retrieved 2021-08-10.
  2. 2.0 2.1 "7 Notable African Women Activists Who Deserve Wikipedia Pages". Global Citizen (in Turanci). Retrieved 2021-08-10. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  3. "Burkina Faso: child marriage puts thousands of girls at grave risk". www.amnesty.org.uk. Retrieved 2021-08-10.
  4. "The women driving change in Burkina Faso". www.amnesty.org.uk. Retrieved 2021-08-10.
  5. Hernández, Hortensia (2016-06-01). "Equal rights for women worldwide: Bibata Ouédraogo". Equal rights for women worldwide. Retrieved 2021-08-10.