Benny Andersen
Benny Andersen (7 Nuwamba 1929 – 16 Agusta 2018) ya kasance marubucin waƙoƙi na harshen Danish, mawaƙi, marubuci kuma mai kaɗa fiyano. An san shi da ayyukansa tare da Povl Dissing . Sun fitar da faifai tare da waƙoƙin Andersen daga tarin Svantes viser .
Benny Andersen | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Benny Allan Andersen |
Haihuwa | Vangede (en) , 7 Nuwamba, 1929 |
ƙasa | Daular Denmark |
Harshen uwa | Danish (en) |
Mutuwa | Sorgenfri (en) , 16 ga Augusta, 2018 |
Makwanci | Assistens Cemetery (en) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Signe Plesner (en) (3 ga Maris, 1950 - 1975) |
Karatu | |
Makaranta | Bakkegårdsskolen (en) |
Harsuna | Danish (en) |
Sana'a | |
Sana'a | maiwaƙe, mai rubuta kiɗa, pianist (en) , marubuci, marubin wasannin kwaykwayo da lyricist (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Kayan kida | piano (en) |
IMDb | nm0026092 |
Wannan kundi da littafin Andersens " Svantes viser " (Wakokin Svante) daga 1972, Ma'aikatar Al'adu ta Denmark ce ta sanya su a Canon Al'adun Danmark a 2006, a cikin rukunin "Mashahurin kiɗa". [1] [2] Andersens " Samlede digte " (Tararrun waƙoƙi) sun sayar da kwafi sama da 100,000 a ƙasar Denmark.
Andersen ya kasance memba na Kwalejin Koyon Danish (Det Danske Akademi) daga 1972 har zuwa rasuwarsa.
Mutuwa
gyara sasheAndersen ya mutu a ranar 16 ga Agusta 2018 a Vangede yana da shekara 88. [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Denstoredanske.dk Kulturkanon
- ↑ Hela den danska Kulturkanonen (in Swedish) Sydsvenskan, retrieved January 20, 2013
- ↑ Benny Andersen er død, BT, 17 August 2018