Benedict Iserom Ita
Benedict Iserom Ita (an haife shi ranar goma ga watan Afrilu 1967) masanin kimiyya ne a kasar Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban Jami'ar Arthur Jarvis tun shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023. [1]
Benedict Iserom Ita | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Cross River, 10 ga Afirilu, 1967 (57 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da Farfesa |
Employers | Jami'ar Arthur Jarvis (2023 - |
An haife shi a ranar 10 ga Afrilu a shekarar alif dari tara da sittin da bakwai 1967 a Aningeje, Akamkpa, Jihar Cross River, Ita ya sami karatun firamare a makarantar firamare ta Presbyterian a Akim Qua Town, Calabar inda ya sami takardar shaidar barin makaranta ta farko a shekarar alif dari tara saba'in da tara 1979 kuma ya ci gaba zuwa Immaculate Conception Seninary a Mfamosing inda ya sami Babban Takardar shaidar Ilimi (GCE) a shekarar alif dari tara da tamanin da hudu 1984.[2] Ita ya ci gaba zuwa Jami'ar Calabar inda ya sami digiri na farko a shekarar alif dari tara da tamanin da tara wato 1989, digiri na biyu a shekarar 1994 da PhD a shekarar 2000 a kan ilimin sunadarai.[2]
Ita Farfesa ce a fannin kimiyyar lissafi kuma ta zama mataimakin shugaban Jami'ar Arthur Jarvis a shekarar 2023.[2]
Bayanan da aka ambata
gyara sashe- ↑ "Vice Chancellor". Arthur Jarvis University.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Benedict Ita Is New Vice Chancellor Of Arthur Jarvis University". Calitown. 11 October 2023. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "Town" defined multiple times with different content