Bashtery Ragel ( Larabci: بشتري راجل‎  ; "Siyan Mutum") wani fim ne na wasan kwaikwayo na soyayya na ƙasar Masar na shekarar 2017, taurarin shirin sun haɗa da Nelly Karim.

Bashtery Ragel
Asali
Lokacin bugawa 2017
Asalin suna بشترى راجل
Asalin harshe Egyptian Arabic (en) Fassara
Ƙasar asali Misra
Characteristics
Genre (en) Fassara comedy film (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Mohamed Ali (en) Fassara
'yan wasa
External links
bashteryragel.com

Halin Karim a shirin yana ƙoƙarin ɗaukar ɗa ta hanyar tambayar wani mutum a dandalin sada zumunta na Facebook. Inas Lofty shine marubucin fim ɗin.[1]

Jagoran shirin a fim ɗin, na gudanar da kasuwanci. Sai ta yanke shawarar cewa ta nemi wani mutum ya ba ta kyautar maniyyi, kuma ta halal sai ta ba da shawarar aure, duk da cewa an yi shi ne kawai don kyautar maniyyi. Mahaifiyarta ta damu da dalilin auren kasancewarsa kasuwanci ne kawai, amma Shams ya fara sha'awar sa sosai, kuma yana yi da matarsa. A ƙarshe suna da ɗa da aka haifa a al'ada. France 24 ta bayyana cewa wannan shine "watakila kawai karshen da zai iya sa fim din yayi nasara tare da masu sauraron Masar".

Yan wasan kwaikwayo

gyara sashe

A cewar marubuciyar fim ɗin, an tsara fim ɗin ne da wata kawarta da take son zama mahaifiya ɗaya kamar yadda take son zumunci amma ba ta da sha’awar auren namiji, saboda ba ta sami kyakkyawar alaƙar soyayya ba.

Tawagar bunƙasa fina-finan ta yi amfani da wani shafin Facebook da ake zargin wata mata ta nemi a ba ta kyautar maniyyi a matsayin wata dabarar talla.[2]

Lofty ya yanke shawarar yin amfani da nau'in wasan barkwanci na soyayya don sa jama'ar Masar su kasance masu dacewa da batun fim din.

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin fina-finan Masar na 2017

Manazarta

gyara sashe
  1. "Sperm donation rom-com is a success in Egypt". France 24. 2017-03-19. Retrieved 2022-01-29.
  2. "Woman seeking sperm donor on FB revealed to be fake for film advert". Egypt Independent. Al-Masry Al-Youm. 2017-01-25. Retrieved 2022-01-29. - This is a translation of an article in Arabic published in Al-Masry Al-Youm, with some editing done to it.

Hanyoyin Hadi na waje

gyara sashe