Babban taron jama'ar Kamaru
Babban taron jama'ar Kamaru (CPNC)jam'iyyar siyasa ce a Kamarun Burtaniya.
Babban taron jama'ar Kamaru | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | jam'iyyar siyasa |
Ƙasa | Kameru |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1960 |
Tarihi
gyara sasheAn kafa CPNC a watan Mayun 1960 ta hanyar haɗewar jam'iyyar Kamerun National Congress da Kamerun People's Party,[1] wadda suka fafata a zaɓen 1959 tare.
Zaben 1961 ya nuna jam’iyyar ta samu kashi 26.8% na kuri’un da aka kada,inda ta samu kujeru 10,kasa da biyu da jam’iyyun biyu suka samu a shekarar 1959.
A zaben farko da aka gudanar a kasar Kamaru dunkule a shekarar 1964,jam'iyyar ta tsaya takara a gabashin Kamaru.Duk da cewa ta samu kashi 24% na kuri'un da aka kada, amma ta kasa samun kujera.[2]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ Mark Dike DeLancey, Rebecca Neh Mbuh & Mark W DeLancey (2010) Historical Dictionary of the Republic of Cameroon, Scarecrow Press, p91
- ↑ Elections in Cameroon African Elections Database