Ayamase
Ayamase, wanda kuma ake kira daAyamashe, wani nau'in miya ne na musamman ko stew wanda ya fito daga ƙabilar Yarbawa a yammacin Afirka. [1] Ana cin shi da shinkafar Ofada, wani lokacin kuma farar shinkafa na yau da kullum. Ana yin shi da barkono, koren barkono da kayan yaji. [2] [3] Yakan ƙunshi nama, kifi da ƙwai. [4] Yana da launin kore mai duhu. Ya sha bamban da miya mai suna Ofada sauce ko kuma stew Lafenwa mai ja kuma ana ci da shinkafar Ofada. [5] Ya shahara a bukukuwan Yarbawa da ake kira Owambe da kuma a cikin girkin gida.
Ayamase | |
---|---|
dish (en) | |
Kayan haɗi | borkono, nama, kifi, Kwai da spice (en) |
Manazarta
gyara sashe- ↑ Uguru, Chichi (2018-01-17). "Ayamase Stew (Designer Green Pepper Stew/Ofada)". My Diaspora Kitchen (in Turanci). Retrieved 2024-03-31.
- ↑ "Ayamase - Ofada Stew". Sisi Jemimah (in Turanci). 2015-08-04. Retrieved 2024-03-31.
- ↑ Osinkolu, Lola (2016-08-05). "How to pepare Ayamase stew (ofada stew)". Chef Lola's Kitchen (in Turanci). Retrieved 2024-03-31.
- ↑ Souldeliciouz (2014-11-01). "How to cook Ayamase (Designer and Ofada) Stew". SOULDELICIOUZ (in Turanci). Retrieved 2024-03-31.
- ↑ Ajoke (2019-11-09). "Ayamase (Designer stew)". My Active Kitchen (in Turanci). Retrieved 2024-03-31.