Auvers-sur-Oise ( furuci da Faransanci: [Ovɛʁ syʁ waz], yana nufin Auvers on Oise ) gari ne a yankin Val-d'Oise, a arewa maso yammacin Paris, Faransa. Garin na da nisan kilomita 27.2 kilometres (16.9 mi) daga tsakiyar Paris. Akwai shahararrun masu zane a garin da dama, mafi mashahuri shine Vincent van Gogh . Wannan shine wurin da van Gogh ya mutu, ga dukkan alamu ta hanyar kashe kansa.

Auvers-sur-Oise


Suna saboda Oise (en) Fassara
Wuri
Map
 49°04′18″N 2°10′27″E / 49.0717°N 2.1742°E / 49.0717; 2.1742
Ƴantacciyar ƙasaFaransa
Administrative territorial entity of France (en) FassaraMetropolitan France (en) Fassara
Region of France (en) FassaraÎle-de-France (en) Fassara
Department of France (en) FassaraVal-d'Oise (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 6,820 (2022)
• Yawan mutane 537.43 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Located in the statistical territorial entity (en) Fassara Q108921672 Fassara
Paris unité urbaine (en) Fassara
Yawan fili 12.69 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Oise (en) Fassara
Altitude (en) Fassara 28 m-21 m-111 m
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Ta biyo baya Butry-sur-Oise (en) Fassara
Tsarin Siyasa
• Mayor of Auvers-sur-Oise (en) Fassara Isabelle Mezières (en) Fassara (28 ga Maris, 2014)
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 95430
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo ville-auverssuroise.fr
hutun Auvers-sur-Oise

Yanayin kasa

gyara sashe

Auvers na nan a bangaren daman kogin Oise . Daga kudu kuwa tana haɗe da Méry-sur-Oise ta hanyar wata gada.Samfuri:Adjacent communities

  • Chaponval
  • Cordeville (daga Corbeville)
  • Le Montcel (daga Monsellus, ƙaramin dutse)
  • Les Vaissenots ko Vessenots
  • Le Valhermeil (daga Val Hermer, sunan mai shi a cikin karni na 12)
  • Les Vallées

A cikin karni na 19, masu zan da dama sunyi rayuwa a garin kuma sun yi aiki a Auvers-sur-Oise, ciki har da Paul Cézanne, Charles-François Daubigny, Camille Pissarro, Jean-Baptiste-Camille Corot, Norbert Goeneutte, da Vincent van Gogh . Gidan Daubigny a yanzu ya zama gidan kayan gargajiya inda mutum zai iya ganin zane-zanen Van Vough, danginsa, da abokansa, irin su Honoré Daumier, da kuma ɗakunan da aka yi wa ado a cikin salo na wancan zamanin. Charles Sprague Pearce (1851-1914) shima anan ya mutu. A gefen kogin daga Auvers zuwa Pontoise akwai wurare da yawa waɗanda ke cikin zanen Pissarro.

A lokacin karni na 20,masu zane sun ci gaba da ziyartar Auvers, ciki har da Henri Rousseau ( Douanier Rousseau ), Otto Freundlich da Pierre Daboval . Mai zane COBRA mai suna Corneille ya shafe shekarunsa na ƙarshe a ƙauyen kuma an binne shi a 'yan mitoci kaɗan daga Vincent van Gogh.[1]

Yawan jama'a

gyara sashe
Historical population
YearPop.±%
17931,754—    
18001,635−6.8%
18061,708+4.5%
18211,705−0.2%
18311,806+5.9%
18361,522−15.7%
18411,530+0.5%
18461,547+1.1%
18511,553+0.4%
18561,574+1.4%
18611,648+4.7%
18661,635−0.8%
18721,720+5.2%
18761,638−4.8%
18811,713+4.6%
18861,936+13.0%
18912,063+6.6%
18962,255+9.3%
19012,402+6.5%
19062,544+5.9%
19112,681+5.4%
19212,961+10.4%
19263,132+5.8%
19313,240+3.4%
19363,163−2.4%
19463,345+5.8%
19543,172−5.2%
19623,772+18.9%
19685,124+35.8%
19755,808+13.3%
19825,722−1.5%
19906,129+7.1%
19996,820+11.3%
20076,917+1.4%
20126,846−1.0%
20176,908+0.9%

A ranar 1 ga Agustan, 1948, an cire kashi 17% na yankin Auvers-sur-Oise kuma ya zama gundumar Butry-sur-Oise .

Magajin garin na yanzu itace Isabelle Mézières. An fara zaɓen ta a shekarar 2014, sannan aka sake zaɓe ta a watan Maris shekara ta 2020.

 
Zauren garin da aka gyara a shekarar 2016

Wuraren tarihi

gyara sashe

Gina cocin ya samo asali ne tun daga ƙarni na 11. Louis VI le Gros (1081-1137) ya mallaki manor a Auvers, inda yakan zo farauta. A shekara ta 1131 dansa Philippe, wanda shi ne yarima mai jiran gado, ya fado daga kan dokinsa ta hanyar kuma ya mutu. An gina ɗakin bauta a wurin da aka binne shi kuma wannan daga baya ya zama cocin Notre-Dame de l'Assomption: a cikin shekarar 1915 wurin ya shiga cikin abubuwan tarihi na duniya. Tare da gidan sarautar, suna wakiltar manyan yankunan tarihi na al'adun birni, inda shahararrun masu zane-zane suka zo a cikin karni na 19, kamar Daubigny, Bourges, Bernard, Pearce, Bastard, Boggio ko Wickenden.

Gidajen tarihi

gyara sashe
  • The musée Daubigny, wanda yake a cikin mazaunin Colombières, an ƙirƙira shi ne a cikin shekarar 1986 wanda Ofishin Yawon Bude idanu suka yi hakan. Gidan kayan tarihin ya kunshi kusan ayyuka dari na Daubigny, kamar zane-zane, fenti da sassake-sassaken sa.
  • Musée de l'absinthe (Absinthe Museum), wanda ke unguwar rue Callé, ya kunshin kayan tarihi na abubuwan sha.

Dr. Paul Gachet ya yi rayuwa a Auvers-sur-Oise. Ya saba da masu zanen avant-garde na lokacin. Ta hanyar wannan alaka, Vincent van Gogh ya koma Auvers don yayi masa magani, kodayake ya iske likitan a cikin wani yanayi mafi muni fiye da yadda yake. Gachet ya yi abota da Van Gogh kuma ya zana hotonsa har sau biyu, daya daga cikinsu, Hoton Dr. Gachet, an sayar da shi a wajen wani gwanjon akan kudi sama da $80m (£48m) a shekara ya 1990.[2]


Van Gogh ya mutu ne sakamakon harbin kansa da yayi a kirji. An adanaa dakin da ya mutu saboda tarihi. Jami'ar Van Gogh ta mallaki Auberge Ravoux, kuma ita ke shirya ziyarar ɗakin Van Gogh kuma ta buɗe gidan cin abinci a dakin.[3] Auvers-sur-Oise shine wurin hutawa na ƙarshe na duka Vincent da ɗan'uwansa Theo van Gogh, wanda ya mutu bayan watanni shida.

Akwai tashoshin jiragen kasa guda biyu a garin Auvers-sur-Oise na Transilien Paris – Nord : Chaponval da Auvers-sur-Oise . Tashoshin duka suna bi ya layin Pontoise - Creil . Tsakanin Afrilu da Oktoba, a ranakun Asabar, Lahadi da ranakun hutu, jiragen kasa kai tsaye suna tafiya daga Paris Gare du Nord zuwa Auvers.

 
Tashar jirgin kasa na Auvers

Hakanan kuma akwai tashoshin bas guda biyu aAuvers : 95 07 da 95 17.

Duba kuma

gyara sashe
  • Ƙungiyoyin sashen Val-d'Oise
  • Auvers a lokacin Vincent van Gogh

Manazarta

gyara sashe
  1. "IVincent van Gogh's Grave". Minor Sights. 14 November 2014. Retrieved 2015-02-28
  2. Dowd, Vincent (24 October 2009). "In the footsteps of Vincent van Gogh". BBC News. Retrieved 2009-10-25.
  3. "Van Gogh in Auvers-sur-Oise. Auberge Ravoux visit". Paris Digest. 2020. Retrieved 2020-07-30.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe